17/08/2026
Takaitaccen Tarihin Najeriya
Najeriya ba kasa bace da aka kirkira jiya. Tarihinta ya fara ne tun dubban shekaru da s**a wuce, kafin ma a samu sunan Najeriya din.
1. Kafin Zuwa Turawa
Kafin turawa su zo, abinda muke kira Najeriya yanzu gida ne ga manyan masarautu da dauloli masu karfi.
A Arewa akwai Daular Kanem-Borno wacce ta yi suna tun karni na 9, da kuma Hausawa Bakwai kamar Kano, Katsina, Zazzau da Gobir, wadanda s**a shahara wajen kasuwanci da ilimin addini. A Yamma kuma akwai Daular Oyo da Benin, wadanda s**a yi fice a harkar jan karfe, zane-zane da gine-gine. A Kudu maso Gabas kuma mutanen Igbo suna da tsarin gudanarwa na gargajiya wanda bashi da sarki daya, kowa na da murya.
Mutane suna noma, kiwo, sana'ar fata, da kasuwanci a fadin Sahara.
2. Lokacin Bauta da Mulkin Mallaka
Turawa na farko da s**a zo su ne Portuguese a karni na 15, amma daga baya Birtaniya ce ta mamaye kasuwancin. Sun fara da fataucin bayi, sai aka koma fataucin manja da gyada.
A karshen karni na 19, Kamfanin Royal Niger Company ya karbe iko da kasuwanci, sai gwamnatin Birtaniya ta karbe shi gaba daya. A shekarar 1914, Lord Frederick Lugard ya hade yankin Arewa da na Kudu ya zama abu daya. Sunan Najeriya din ma matar Lugard, Flora Shaw ce ta bada shawara, daga kalmar Niger.
3. Hanyar Samun 'Yanci
Bayan yakin duniya na biyu, 'yan Najeriya s**a fara neman 'yanci. Manyan mutane kamar Herbert Macaulay, Nnamdi Azikiwe, Obafemi Awolowo da Sir Ahmadu Bello s**a jagoranci jam'iyyu s**a wayar da kan mutane.
Daga karshe a ranar 1 ga Oktoba, 1960, Najeriya ta samu 'yancin kai daga Birtaniya. Tafawa Balewa ya zama Firaminista na farko, Azikiwe kuma Gwamna Janar.
4. Bayan 'Yanci Zuwa Yau
Shekarun farko bayan 'yanci basu yi sauki ba. Akwai bambancin kabila da siyasa. Wannan ne ya kai ga juyin mulkin soja na farko a 1966, wanda ya kashe Ahmadu Bello da Tafawa Balewa. Bayan haka rikici ya barke, wanda ya kai ga Yakin Basasa na Biafra daga 1967 zuwa 1970, lokacin da Chukwuemeka Ojukwu ya yi yunkurin ra