Bbc Street Hayin Ojo Sabon Gari Zaria

Bbc Street Hayin Ojo Sabon Gari Zaria Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Bbc Street Hayin Ojo Sabon Gari Zaria, Photographer, Zaria.

Inayiwa daukacin al'ummar Hayin Ojo musamman na layin Alhaji Rabi'u Bbc barka da wannan wata mai albarka, Allah yasada m...
07/05/2021

Inayiwa daukacin al'ummar Hayin Ojo musamman na layin Alhaji Rabi'u Bbc barka da wannan wata mai albarka, Allah yasada mu da alkhairan dake cikinsa mussaman Daren lailatul qadri.Amin.

27/12/2017

KULLU NAFSIN ZAIKATUL MAUT
ADARAN JIYANE ALLAH YAYIWA MAI GANDA (SARKIN YAN TUKWANE HAYIN OJO SABON GARI LOCAL GOVERNMENT) RASUWA WANDA AKAYI JANAZARSA DA MISALIN KARFE 9:00 NASAFEN 27/12/2017 ALLAH YA JIKANSA DA RAHAMARSA AMIN

16/11/2017

# ALHAMDULILLAH #
All praise is due to Allah the creator of everything, it is he who bestows his mercy to whom he wishes without consultation from anyone.Therefore this is to inform you (brothers and sisters) that my law school admission has finally been released yesterday Wednesday 15th of November, 2017 and I have been successfully posted to Kano(bagauda) Campus, I therefore solicit your prayers thanks.

14/11/2017

ASSALAMU ALAIKUM
# # #
Ina mai farin cikin sanar da 'yan'uwa da abokan arzuka musamman al'ummar garin hayin Ojo da kewaye cewa insha Allahu gata Juma'a za'a gudanar da sallar juma'a wacce aka saba gudanarwa a masallacin Government commercial college zaria a masallacin Alhaji Rabi'u B b c dake kofar gidansa, kuma daga rannan za'a cigaba da gudanar da sallar juma'ar anan masallacin na Alhaji Rabi'u B b c .Canjin masallacin yabiyo bayan la'akari da wasu dalilai masu qarfi acikin addinin musulunci, domin jin dalilan saika halarci masallacin a gata juma'a a inda mahukuntan masallacin zasu bayyana, Allah ubangiji yabada ikon halarta amin.

15/08/2017

Law school admission is loading 85%, may Allah (Swt) make the best choice for us amin.

 #  WA INNA ILAIHI RAJI'UN  # #Allah ina roqonka kajiqan Dr.Alhaji, Yusuf Maitama Sule (Dan Masanin Kano), kasa Aljannah...
09/07/2017

# WA INNA ILAIHI RAJI'UN # #
Allah ina roqonka kajiqan Dr.Alhaji, Yusuf Maitama Sule (Dan Masanin Kano), kasa Aljannah tazama makoma agareshi amin.
kafin marigayin ya rasu yakasance idan yaje taro ko wani abu mai k**a da haka yakanyiwa Allah (Swt)kirari k**ar haka:
"BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM.
GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI, MAI KOWA, MAI KOMAI, MAI YADDA YA SO, KAN WANDA YA SO, YAYIN DA YA SO, A INDA YA SO, KO ANA SO, KO BA A SO.
GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI MAI BAWA KOWA KOMAI, BA SHIDA BUKATAR KOMAI A GURIN KOWA, KOWA KE DA BUKATAR KOMAI A GURINSA.
MAMALLAKIN MAMALLAKA, MAI BADA MULKI GA WANDA YASO, YA FUZGE DAGA WANDA YASO, YA DAUKAKI WANDA YASO, YA KASKANTAR DA WANDA YA SO, LILLAHI WAHIDIL KAHHAR.
SARKIN DA BA SHI DA NAN, BALLANTANA YA YI NAN, BA SHI DA CAN, BALLANTANA YA YI CAN, A KO INA YANA NAN.
NA FARKO NE BA DA FARAWA BA, NA KARSHE NE BA DA KAREWA BA, A BAYYANE YA KE BA A GANINSA, A BOYE YA KE BA DON BA YA NAN BA.
SARKIN DA YA KASANCE TUN KAFIN KASANCE WA TA KASANCE, KUMA ZAI KASANCE BAYAN KASANCEWA TA GUSHE DA KASANCEWA. LILLAHI WAHIDUL KAHHAR".
Allah ya jikan Dan masanin Kano.Amin.

21/05/2017

"TSOKANA"
Wani Bafulatani ne Babarsa Ta
mutu sai sarkin fawa s**aje yi
masa Ta'aziya Bayan sun gaisa
sai Sarkin Fawa yacewa
Bafulatanin saikayi hakuri
kasan rashin uwa Babban
rashine Sai bafulatanin yace
Haba Sarkin Fawa to Saniya Da
Ciki ma ta mutu mukayi hakuri
b***e Inna.

23/04/2017

# # FATAWA # #
Assalamu Alaikum, wata rana anyiwa Malam Dr.Jamilu zarewa tambaya kuma ya amsa k**ar haka:
Assalamu Alaikum. Dr ko ya halatta Musulmi yayi wa dan'uwansa murna da zagayowar juma'a ta hanyar sako a wayar sailula k**ar ace JUMA'A KAREEM ko JUMA'A MUBARAK? Allah yaqara sani.
Amsa:
Wa alaikum assalam, Akwai malaman da su ka hana hakan, suna ganin ba shi da asali a addini, Amma abin da yake zahiri hakan ya fi k**a da al'ada, wannan yasa haramta shi yake bukatar Nassi, tun da babin al'adu da mu'amaloli a bude yake, sai abin da sharia ta haramta. Duk Wanda yake yi ba tare da ya riya cewa ibada ba ce hana shi ko bidi'antar da aikinsa yana da wuya, k**ar yadda Ibnu Uthaimin ya yi nuni zuwa haka a fatawar da aka yi masa.
Saidai duk da haka ya k**ata kar Musulmi ya zamar da shi al-adarsa kowace juma'a, don kar wasu su fahimci ibada ne.
Allah ne mafi sani
23/10/2016
DR JAMILU ZAREWA

22/04/2017

# # JAN HANKALI 2 # #
slm,yakai dan'uwa mai karamci meyasa kake zaton cewa wani dan'uwanka yana cin namanka (gulmarka ko munafincinka) duk dacewa baka da hujja face kawai son rai? Bakasan cewa manzon tsira yace"iyyakum wadhdhanna fa'innadhdhanna akdhabul hadith" ma'ana"nahaneku dayin zato domin shi zato labari na qarya".Har ilayau manyan malamai suna cewa"adhdhanna dhambun walau kana haqqun" ma'ana"zato zunubi ne koda yakasance gaskiya ne".To,yakai dan'uwa mezai hana ka nisanci yin zato don samun tsira gobe qiyama? Fatanmu har kullum Allah Swt ya bamu ikon yimasa biyayya kuma ya bamu ikon yiwa manzon Allah biyayya don kasancewa cikin wanda zasu rabauta duniya da lahira amin. Barkanku da Safiya da fatan Allah yasada mu da rahamarsa awannan rana yakuma karemu daga musibun dake cikin wannan rana amin.

02/03/2017

# # YADDA GARIN HAYIN OJO YASAMO ASALI # #
To,labari ya ishemu cewa garin hayin ojo a yanzu ada ya kasance wani tsibiri ne ko kuma ince tudu ne wanda kafin mutum ya isa sai ya haye/haura wani tafki/kogi ,bayan haka babu kowa awajen sai gonaki ,kawai wataran sai wani mutum mai suna ojo ya yanke shawarar yin matsuguni awajen inda ya gyara gonarsa yayi bukka ya tare amazaunin gidansa wanda daka baya yayi ginin qasa, labari ya ishemu cewa jim kadan bayan tarewar ojo sai mutane masu gonaki a hayin s**a fara hayawa suna gina gonakinsu suma amatsayin gidaddaji.Yakasance alokacin da s**a fara ginin duk sanda zasu je sai s**e da juna kuzo muje hayin ojo. Kaji yadda sunan hayin ojo ya samo asali, dafatan ka gamsu

28/02/2017

ASSALAMU ALAIKUM***
Ajiya ne Allah Swt ya qaddarawa kawuna (yayan mahaifiyata) yin hatsari, kawunnawa Wanda akafi sani da Alhaji Rabi'u b b c dake zaune a hayin Ojo karamar hukumar sabon gari dake garin zaria, hatsarin ya auku ne akan hanyarsa ta dawowa gida daga flyover (kwangila duk a qaramar hukumar ta sabon gari, take aka garzaya dashi Babban asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello dake shika zaria a inda yanzu haka yake karbar ingantacciyar kulawa kuma al'amarin yazo da sauki.A qarshe muna roqon. 'yan'uwa susa kawunnamu cikin addu'a Allah Swt yabashi lafiya, Allah yasa kaffara ne bisa ingantacce hadisi Wanda aka ruwaito manzon Allah yace"Babu wata musiba da zata shafi mumini face Allah ya kankare masa zunubansa, ya Allah muna rokonka da sunayenka kyawawa da suffofinka tsarkaka kaba shi lafiya kasa hakan yazama sanadiyyar kubutarsa damu daga azabar wuta kuma kasa hakan yazama sanadiyyar shigarsa damu baki daya gidan aljannah amin.

20/02/2017

# # # MURNAR MUTUWA MURNAR BANZA # # #
wai masu murna cewa Allah yasa shugaban qasa Malam Muhammad Buhari ya mutu a can karya dawo Najeriya,to munji yamutu kai/ke kuma idan kai/ke kike/kake da iko akan rayuwarka/rayuwarki ka/ki zauna jiran duniya karka/ki mutu shashasha kawai marasa tunani,zindiqai, jahilai, 'yan bidi'a Kanku akeji to idan yamutu meye ribarku? kudaiyi mugani wallahi sai kunji kunya wawaye masu bakar siffa da bakar sutura da bakar zuciya wahala bata qare muku ba.Aqarshe inaso kusani cewa duk makircin mai makirci bai isa yayiwa kowa komai ba face abin da Allah ya qaddara akansa , don haka mai makirci yayi tayi Allah yana ganinsa kuma bazaici nasara ba har abada saidai wahala wata kan wata.

Address

Zaria

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bbc Street Hayin Ojo Sabon Gari Zaria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category