06/01/2026
SHAWARORI NA MUSAMMAN DAGA MANYA
👇
1 - A rayuwa bakomai zai faru kamar
‎yadda ka tsara ba. Saboda haka ka rage tsammani, ka bi yadda rayuwa ke tafiya.
‎
‎2 - Ka rage bakin ciki da ƙiyayya a rayuwarka, domin hakan na jinkirta albarka.
‎
‎3 - Soyayya da mace mai goyon bayanka akan cinma muradanka, abu ne mai matuƙar muhimmanci.
‎
‎4 - Ka bi burinka, ba mutane ba.
‎
‎5 - Ka yi magana ne kawai idan maganarka ta fi shiru kyau.