24/07/2026
SHUGABANNIN MATA NA ADC A JIHAR BORNO SUNA TAYA MURNA GA ALH MAMMAN DAUDA KACHALLAH, SUN YI ALKAWARIN TABBATAR DA NASARAR TIKITIN BABAGANA/MAMMAN A 2027.
A madadin ɗaukacin Shugabannin Mata na Jam'iyyar ADC a Jihar Borno, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Maryam Ibrahim Imam, muna bayyana matuƙar farin cikinmu tare da taya Mai Girma Alhaji Mamman Dauda Kachallah murnar amincewar da Mai Girma Gwamnan Jihar Borno da yardan Allah, Alhaji Babagana Buhari, ya sake nuna masa ta hanyar tabbatar da shi a matsayin abokin takararsa a zaɓen Gwamnan Jihar Borno na shekarar 2027.
Mun yi imanin cewa wannan amincewa ta samo asali ne daga irin aminci, jajircewa, ƙwarewa da sadaukarwar da Alhaji Dauda Mamman Kachallah ya nuna wajen gudanar da ayyukan jami'iyyar da kuma hidimtawa al'ummar Jihar Borno.
Haka kuma, muna miƙa saƙon godiya ta musamman ga Mai Girma Gwamna Alhaji Babagana Buhari bisa wannan mataki, wanda ya nuna muhimmancin amana, biyayya da aiki tuƙuru a cikin shugabanci.
A matsayinmu na shugabannin mata na ADC a faɗin ƙananan hukumomi 27 da Mazaɓu 312 na Jihar Borno, muna tabbatar da cewa za mu ci gaba da haɗa kan mata, wayar da kan masu kaɗa ƙuri'a, da kuma gudanar da ayyukan siyasa cikin lumana domin tabbatar da nasarar wannan tikiti a babban zaɓen shekarar 2027, In Sha Allah.
Muna kira ga ɗaukacin al'ummar Jihar Borno da duk masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da su ci gaba da ba da fifiko ga haɗin kai, zaman lafiya da ci gaban jam'iyyar ADC da jihar mu ta Borno baki daya.
Muna addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya ci gaba da ba shugabanninmu hikima, lafiya da ikon sauke nauyin da ke kansu, tare da ba su nasara a dukkan al'amuransu.
Hajiya Maryam Ibrahim Imam
Shugabar Mata, Jam'iyyar ADC, Jihar Borno.
A Madadin:
Daukacin Shugabannin Mata na Jam'iyyar ADC, Jihar Borno.
Comr Hussaini Kambar
24th July 2026.
Official Page of Hajiya Maryam Ibrahim Imam | State Women Leader ADC Borno State. Advocate of women's political empowerment and grassroots mobilization. Dedicated to inclusive leadership, unity, peace, and sustainable development.