Masarautar kontagora mai Sudan na bakwai

Masarautar kontagora mai Sudan na bakwai Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Masarautar kontagora mai Sudan na bakwai, Camera/Photo, Kontagora.

19/02/2024
*MAI MARTABA SARKIN SUDAN YA TABBATAR WA HAKIMIN MASUGA ALH. ATIKU ISAH IBRAHIM DA SARAUTAR SARKIN GOBIR.*Mai martaba Sa...
19/02/2024

*MAI MARTABA SARKIN SUDAN YA TABBATAR WA HAKIMIN MASUGA ALH. ATIKU ISAH IBRAHIM DA SARAUTAR SARKIN GOBIR.*

Mai martaba Sarkin Sudan Kontagora Alh Muhammadu Barau Mu'azu II ya tabbatar wa Hakimin sa da Sarautar *"SARKIN GOBIR KONTAGORA".*

Sarkin Gobir sarauta ce mai da ɗadden asali a masarautar arewa, wanda ba a baiwa raggo wannan Sarautar sai jajurtace.

Mai martaba Sarkin Sudan ya bada wannan sarautar a inda ta dace.

Allah ya tabbatar da alkhairi yasa rayuwa ak**a ya jagorance ka akan wannan sarautar amin.

MAJALISAR SARAKUNAN JAHOHIN AREWA 19 SUNGUDANAR DA TARO DAYASHAFI MATSALAR TSARO A AREWA HOUSE KADUNA.Ajiya Larba 14th F...
15/02/2024

MAJALISAR SARAKUNAN JAHOHIN AREWA 19 SUNGUDANAR DA TARO DAYASHAFI MATSALAR TSARO A AREWA HOUSE KADUNA.

Ajiya Larba 14th Feb, 2024 Mai martaba Sarkin Sudan Alh Muhammadu Barau Mu'azu II, ya halarci taron Sarakunan Arewa a dakin taro na Arewa House dake Kaduna, Mai martaba Sarkin Sudan ya wakilci Etsu Nupe Alh Yahaya Abubakar Shugaban majalisar sarakunan gargajiya na Jahar Neja.

Taron mai taken " HANYOYIN SHAWO KAN RASHIN TSARO WANDA HAKAN KE KAWO TAƁARƁAREWA DA KOMA BAYAN AREWA" an gudanar da taron ne a karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Dr. Muhammad Sa'ad Abubakar III.

Bayan lamarin tsaro, sarakunan sun tattauna kan abinda ya shafi tsadar rayuwa dake addabar al'ummar yankin arewa.

Allah ya temaki sarakunan mu ya basu ikon shawo kan waɗannan matsalolin da s**ayi katutu a Arewa.

Allah ya dawo muna da zaman lafiya a ƙasar mu Najeriya tare da ƙaruwar arziki a yankunan mu amin 🤲

*TAKARDAR DAKATAR DA SARAUTAR YARIMAN KONTAGORA* Amadadin Ƴan'majalisar Sarkin Sudan Kontagora na sanar da janye sarauta...
21/12/2023

*TAKARDAR DAKATAR DA SARAUTAR YARIMAN KONTAGORA*

Amadadin Ƴan'majalisar Sarkin Sudan Kontagora na sanar da janye sarautar Yariman Kontagora daga hannun Shehu Sa'idu Namaska daga Talata 19th December, 2023.

Majalisar Sarkin Sudan na godiya bisa ƙoƙarin da ya bayar a baya.

Allah ya ƙarowa masarauta albarka ya ƙara bamu jajurtattun shugabani masu hikima da adala wajen kawo cigaba da kwanciyar hankali a wannan masarautar amin 🤲

SANARWA!!!!!!!!!! SANARWA!!!!!!!!!!!!SANARWA.MAI MARTABA SARKIN SUDAN YA JA LAYI KAN HAWA IDIN WASU AL'UMMA BAYAN MAI AL...
16/12/2023

SANARWA!!!!!!!!!! SANARWA!!!!!!!!!!!!SANARWA.

MAI MARTABA SARKIN SUDAN YA JA LAYI KAN HAWA IDIN WASU AL'UMMA BAYAN MAI ALFARMA SARKIN MUSULMI YA SANAR DA GANIN WATA ƘARAMA KO BABBAR SALLAH.

A zaman fada na yau Asabar 16th Dec, 2023, Mai martaba Sarkin Sudan Kontagora Alh Muhammadu Barau Mu'azu II tare da ƴan'majalisa sun dauƙi matsaya ɗaya kan Tungan Sani ~ ƙarƙashin kulho Ƙaramar hukumar Mashegu dama sauran garuruwan dake ƙarƙashin masarautar Kontagora kan ƙin hawa sallar idi ranar da Mai martaba Sarkin Sudan ya hau sallah.

Wannan hukuncin ya biyo bayan ƙarar da aka kawo ne na Malama Abdullahi shugaban wata kungiyar da ke iƙrarin YAN'SAISUNGANI ko ƳAN'SALAWUDDIN da ya bijirewa wasu ƙa'idojin da s**a saɓawa masarauta da addinin Muslunci.

Mai martaba Sarkin Sudan ya zartar da hukuncin ne gaban Jami'an tsaro ciki harda na fararen kaya, sannan masarauta zata cigaba da bibiyar dukkan lamurran su dun ganin basu saɓawa hukuncin da masarauta ta ɗauka akan su ba.

Aƙarshe Mai martaba Sarkin Sudan ya umurci shi shugaban su Malam Abdullahi da yakawo mashi shaidar takardar sa ta zama Ɗan'ƙasa, domin bayanai sun zo ma masarauta cewar shi Malam Abdullahi ba Ɗan'ƙasa bane.

Masarautar Kontagora na yaƙi da rashin *GASKIYA/ADALCI* da kuma bijirewa umurnin shugabanni matuƙar suna kan gaskiya. Sannan Mai martaba na tsaye ƙyem kan adalci koda kuwa wakilan shi aka sama da rashin adalci yasha alwashin hukunta su, dun hakan adalci.

Allah ya zaunar muna da ƙasa lafiya ya saukar muna da arziki ya yaye mana dukkan wata fitina amin 🤲.

Allah ya temaki Sarkin Sudan da ƴan'majalisar shi akan daidai yayin zartar da hukunci ya kuma basu ikon adalci amin 🤲

EMIRATE MEDIA #

An kaddamar da Alhaji Muhammadu Barau Mu'azu na II, Sarkin Sudan na kontagora amatsayin sabon shugaban jami'ar kimiyya d...
01/12/2023

An kaddamar da Alhaji Muhammadu Barau Mu'azu na II, Sarkin Sudan na kontagora amatsayin sabon shugaban jami'ar kimiyya da fasaha dake Ikot Abasi (FUTIA).

Akwanakin bayanedai shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu ya ayyana sarkin Sudan Alhaji Muhammadu Barau Mu'azu na II, tare da bashi takardan k**a aiki amatsayin shugaban jami'ar.

Muna fatan Allah yatayashi riko, yamashi jagora wajen shugabanci.

Emirate Media #

A yau ne 30-11-2023 jami'ar fasaha dake Ikot Abasi (FUTIA) zatayi bikin yaye dalibai, Kuma akaron farko shugaban jami'ar...
30/11/2023

A yau ne 30-11-2023 jami'ar fasaha dake Ikot Abasi (FUTIA) zatayi bikin yaye dalibai, Kuma akaron farko shugaban jami'ar na farko Maimartaba sarkin Sudan Alhaji Muhammadu Barau Mu'azu na II, shine zaijagoranci bikin.

Munafatan Allah yasa ayi wannan taro lafiya akuma gama lafiya, Allah yakarawa maimartaba lafiya.

Emirate Media #

MAI MARTARBA SARKIN SUDAN YA KIRA ZAMAN SULHU TSAKANIN AL'UMMAR GUNDUMAR SALKA DA DAGACIN SU.Masarauta wata Kotu ce ta a...
10/11/2023

MAI MARTARBA SARKIN SUDAN YA KIRA ZAMAN SULHU TSAKANIN AL'UMMAR GUNDUMAR SALKA DA DAGACIN SU.

Masarauta wata Kotu ce ta adalci wajen sasanci dun tabbatuwar zaman lafiya tsakanin al'umma ba tareda bambancin yare ko addini ba.

Mai martaba Sarkin Sudan Alh Muhammadu Barau Mu'azu II ya gayyaci Hakimin Salka tareda Kabilun Kambarin da sauran jama'ar dake goyan baya Dagacin Salka Alh. Abara da ɗaya ɓangaren masu husuma dun kawo ƙarshen wannan fitinar da abaya takai ga hasarar dukiyoyi da ƙone ƙone gidaje da office din Ƴan'sanda.

Mai martaba Sarkin Sudan ya kuma gayyaci Jami'an tsaro dun shigowa dasu ciki domin samun maslaha, sai dai ayau juma'a ɗaya ɓangaren basu sami halartan Fadar Mai martaba Sarkin Sudan ba, sai dai wata takardar da s**a gabatar wa Fada tareda sa hannun waɗan da ke neman a chanza Dagacin, sai dai angano acikin takardar wasu daga sunayen da aka gabatar basu da masaniyar dun kuwa akwai wasu daga cikin waɗan da s**a halarci Fadar ayau sun tabbatar wa Fada wannan takardar ba da masaniyar su aka gabatar da ita ba.

Wakilin Doka kuma Area Commander Gawuna da area commander DSS da CIB sun nemi masarauta tabasu damar yin binkicen abinda ke ciki tareda ladabatar da waɗan da keda hannu ciki dun neman tada tarzoma a tsakanin al'umma.

Mai martaba Sarkin Sudan ya aminta kuma ya ba Hakimi wata damar ƙarshe dun tara al'ummar Salka da su zauna lafiya domin duk inda ya k**ata yayi binkice akan ƙorafe ƙorafen su yayi ba a sami Dagacin Salka Alh. Abara da wani laifi ba.

Mai martaba Sarkin Sudan ya yi rantsuwa da ya same shi da wani laifi da ya warware mashi rawani ba tareda bata lokaci ba, amma Hakimin Salka yaje ya tara al'ummar shi ya isar da saƙon shi gare su.

Kafin rufe zaman Mai martaba Sarkin Sudan ya umurci daga cikin Kirista da Musulmai asami mutane biyu - biyu dun jin ta bakin su. Haka kuma akayi daga ciki harda shugaban mata Mrs. Esta da aka sa sunan ta, ta musanta tareda yin Allah ya isa da saka sunan ta tace ita zaman lafiya take nema, kuma tana neman abasu Dagacin Salka dun su koma gida tare.

Aƙarshe dai Mai martaba Sarkin Sudan ya ƙara basu hankuri da su koma gida kuma a zauna lafiya sannan su bari a ƙarƙare binkice akan matsalar zasuji sak**ako insha Allah.

Sarkin adalci Mai martaba Allah yama tsawon rai tareda ƙoshin lafiya ya ƙara ma hikima da adalci wajen zartar da hukunci amin 🤲
EMIRATE MEDIA #

*MAI MARTARBA SARKIN SUDAN YA KIRA ZAMAN GAGGAWA DA DUK MAI RUWA DA TSAKI KAN TSARO A MASARAUTAR KONTAGORA.*A ƙoƙarin da...
10/11/2023

*MAI MARTARBA SARKIN SUDAN YA KIRA ZAMAN GAGGAWA DA DUK MAI RUWA DA TSAKI KAN TSARO A MASARAUTAR KONTAGORA.*

A ƙoƙarin da Mai martaba Sarkin Sudan Alh Muhammadu Barau Mu'azu II ke yi ƙarkashin ƙasa dun magance matsalar tsaro na manyan yan'taddan da s**a addabi wannan yankin sai ga kuma wata fitinar na nemar dawowa ta yan'sara s**a a wasu unguwanni dake cikin Kontagora.

Mai martaba Sarkin Sudan baiyi ƙasa a guiwa ba wajen kiran duk wani mai ruwa da tsaki tun daga masu kaki, Lauyoyi, Yan'siyasa, Malamai da sarakunan masarautar shi kan shawo kan wannan matsalar ta Sara s**a dun murƙusheta baki ɗaya.

Sanin kowa ne sha'anin tsaro sirran ta shi akeyi, duk da dai Madawakin Kontagora Alh. Aminu Ahmed ya alakanta hakan da sakacin masu unguwanni da Dagatai dun suke da hakkin sannan al'ummar dake tare da su. Haka ma Dillalan filaye da gidaje na da nasu gudun mawa wajen sai da wa kowa yazo da kudin shi fili ko gida ba tareda binkice ba.

Akarshe dai Shamakin Kontagora ya bada shawara kasancewar shi na ƙwararen lauya kuma mai baiwa masarauta shawara dun ɗaukar ƙwaƙ'ƙwaran matakai batare da bata lokaci ba.

Mai martaba Sarkin Sudan ya sha alwashin bada duk wata gudunmawa na ganin talakawa sunyi barci da idanun su biyu a rufe, dun babu wanda yafi karfin doka, dun haka ne Mai martaba Sarkin Sudan ya bukaci shigo da alkalai dun gaggauta fitar da dokan da zaiyi dai'dai da wannan laifin

Allah ya temaki Sarkin mu da ƴan'majalisar shi akan wannan namijin ƙoƙarin tareda sauran dukkan mai wata gudun mawa da hakan zai haifar da samun tsaro da kwanciyar hankali tsakanin al'ummar masarautar Kontagora amin.

EMIRATE MEDIA #

Address

Kontagora

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Masarautar kontagora mai Sudan na bakwai posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category