05/06/2026
PART 5 – Tambayoyi
A cibiyar bincike, jami'ai s**a fara yi wa Magajiya tambayoyi.
Wa ka kai masa kwanaki uku kafin mutuwarsa?
Magajiya ta yi shiru.
Jamcy.
Yanzu ina take?
Ban sani ba.
Jami'an s**a gano cewa an tura wa Jamcy kuɗi masu yawa.
Amma babu wani bayani da ya nuna inda ta nufa.
A hankali Magajiya ta fara tsoron cewa ita ce za ta ɗauki laifin abin da ba ta aikata ba.
PART 6 – Sirrin Jamcy
Bayan dogon bincike, jami'ai s**a gano cewa Jamcy tana amfani da sunaye daban-daban a wurare daban-daban.
Ba k**ar yadda kowa yake tunani ba.
Jamcy ba yarinya ce mai sauƙin yaudara ba.Ta daɗe tana tattara bayanai a kan wasu manyan mutane masu aikata laifuka a ɓoye.
Tun da farko ta yi zargin cewa ana son amfani da ita a wani shiri.
Saboda haka ta shirya kanta.
Ta ɗauki matakan kariya kafin ta je ganawar.
Lokacin da ta fahimci hatsarin da take ciki, sai ta ɓace.
Amma har yanzu ba a san ko tana da alaƙa da mutuwar ɗan siyasar ba.
PART 7 – Gaskiyar da Ta Girgiza Kowa
Daga ƙarshe wani tsohon almajirin bokan ya bayyana wa jami'ai wani sirri.
Ya bayyana cewa bokan ya daɗe yana damfarar ɗan siyasar da ƙarya da tsoratarwa.
Lokacin da bokan ya ga abubuwa ba su tafi yadda yake so ba, sai ya tsoratar da shi cewa mutuwa za ta zo.
A binciken likitoci kuwa...
An gano cewa ɗan siyasar ya mutu ne sak**akon wata matsananciyar matsalar lafiya da ya daɗe yana ɓoye wa mutane.Ba a samu wata shaida da ke nuna cewa Jamcy ta kashe shi ba.
An saki Magajiya.
Amma Jamcy ba ta sake bayyana ba.
Shekara guda bayan haka...
Wata mata ta sauka daga mota a wani gari mai nisa.
Ta sa tabarau baki.
Ta kalli wani ginin gwamnati sannan ta yi murmushi.
Mutanen garin sun san ta da wani sabon suna.
Amma masu karatu sun san gaskiya.
Jamcy tana raye.
Kuma har yanzu tana ɓoye wasu sirrika da ba a tona ba...
ƘARSHEN LABARI. Wannan shine karshen labarin se mun hadu a wani labarin sai anjima 👋🎬