Yaks Idris Bamalli Zazzau Emirates photographer

Yaks Idris Bamalli Zazzau Emirates photographer Yaks Idris BAMALLI

🎉 I earned the fan favorite badge this week, recognizing me for consistently having meaningful conversations with my fan...
26/08/2026

🎉 I earned the fan favorite badge this week, recognizing me for consistently having meaningful conversations with my fans while sharing unique, relatable content!

Laraba, Rabi'ul Awwal 13, 1448AH Wednesday, August 26, 2026DAGA MASARAUTAR  ZAZZAU:-AN KARRAMA MAI MARTABA SARKIN ZAZZAU...
26/08/2026

Laraba, Rabi'ul Awwal 13, 1448AH
Wednesday, August 26, 2026

DAGA MASARAUTAR ZAZZAU:-

AN KARRAMA MAI MARTABA SARKIN ZAZZAU DA LIYAFAN GIRMAMAWA

Rahoto, ABDULLAHI ALIYU KWARBAI

A yau an gudanar da liyafan karramawa na musamman ga Mai Girma Sarkin Zazzau Shugaban Majalisar Sarakuna Jihar Kaduna, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR, a Warri, na Jihar Delta.

Durbin Zazzau, Alhaji Muhammad Aminu Aliyu Bamalli, da Jarman Zazzau, Alhaji Muktar Shehu Ibrahim, tare da yaran Sarki ne s**a raka Mai Martaba Sarki Zazzau a wannan ziyara.

Liyafan girmamawan ya bai wa sarakuna da masu ruwa da tsaki a Jihar Delta damar tattaunawa da Mai Martaba Sarkin Zazzau, tare da jaddada muhimmancin hadin kai, musayar al’adu, da zaman lafiya tsakanin ‘yan Nijeriya baki daya.

Muna addu'an Allah Ya dawo mana da Mai Martaba Sarkin Zazzau da 'yan rakiyansa gida lafiya bayan kamalla wannan ziyara.

Yada Labarai, na Masarautar Zazzau

25/08/2026

Tambaya ? Dazu Nazo Wucewa Naga Wasu Mutane Nata Muhawara Akan Wai Tsakanin Yaran Masu Kudi Da Yaran Talakawa Acikinsu Waye Yake Bata Wani?

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Zunnurain Shehu Usman, Rabeel Bunza, Umar Isah, Musa Alha...
25/08/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Zunnurain Shehu Usman, Rabeel Bunza, Umar Isah, Musa Alhassan, Sarki Shehu Dangorubn Misau, Abdul Azeez Sunusi Shehu, Yushau Ahmed, Umar Farouq Mafara, Adamu Abubakar Jibrin, Luka Asemka, Ahmad Tijjani Jume, Ibrahim Babangida Adamu, Abubakar Idris Ahmed Hadejia, Mohammed Haruna, Mohammed Bashir, Fatimatu Talatu Usman, Comr Saliss Rabi'u-Ali Zuntu, Nuraddeen Lawal, Bello Abdul, Muhammed Bako, Audu Sani Potiskum, Salisu Roba, Nurah Ahmad Bala, Suleiman Attahiru, Basheer Ahmad, Mansur Ahmed Yarin Faru, Safayanu Sani, Muhammad Rasheed, Dahiru Dankwara Adamu, Lawal Nafiu Abdulsalam Aljajawi, Jamilu Hassan, Hadi Yakubu Adamu, Musa Muhammad, Habibu Aliyu, Nura Shafiu Muhammad, Usman Abdullahi Ibrahim, Muhammad Abba, Abubakar Ahmad, Tahir Aminu Bako, Safiyanu Muhammad Sani, Usman Aliyu, Haruna Sani Wagula, Magaji Maigari Madara, Abdourlqadeer Athamou Muhammad, Ramadan Ibrahim, Abdul Shuaib, Bashir Abba Kormi, Musa Eleojo, Mustapha Adam Musty, Yusif Biniya

08031957267
25/08/2026

08031957267

Zazzau  Zazzau                        Happy MAULID     Munama  Daukacin Al'ummar Musulmin Fadin Duniya  Fatan Alkairi Da...
25/08/2026

Zazzau Zazzau

Happy MAULID

Munama Daukacin Al'ummar Musulmin Fadin Duniya Fatan Alkairi Da Wannan Rana

Talata, Rabi'ul Awwal 12, 1448AH Tuesday,  August 25, 2026 DAGA MASARAUTAR ZAZZAU:-AN GUDANAR DA BIKIN MAULIDI A MASARAU...
25/08/2026

Talata, Rabi'ul Awwal 12, 1448AH
Tuesday, August 25, 2026

DAGA MASARAUTAR ZAZZAU:-

AN GUDANAR DA BIKIN MAULIDI A MASARAUTAN ZAZZAU

Rahoto, ABDULLAHI ALIYU KWARBAI

Yayin da Musulmi a fadin duniya ke Bikin murnar tunawa da haihuwar Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad S.A.W, Masarautar Zazzau a yau ta gudanar da addu'o'i na musamman, da jawabai, masu ban sha’awa bisa rayuwan Annabi Muhammadu S.A.W

A gidan Sarkin Ladannan Zazzau, Sarkin Fadar Zazzau, Alhaji Abbas Ahmed Fatika, 'Dan Majalisa a Masarautar, ne ya wakilci Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR, Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kaduna a wajen gudanar da addu'o'in.

Sarkin Fada Zazzau ya jagoranci, 'yan Majalisa, da Hakimai, da manyan malamai, gami da dubban al’ummar Musulmi wajen gudanar da addu'o'in.

A cikin sakon da ya isar a madadin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Sarkin Fadan Zazzau ya yi kira ga Musulmi da su yi koyi da kyawawan dabi’un Annabi Muhammad S.A.W na hakuri, tausayi, da gaskiya.

Ya ce: “Rayuwar Annabi jagora ce cikakkiya ga bil’adama. Yayin da muke murnar ranar haihuwarsa, ya kamata mu yi tunani kan koyarwar sa ta zaman lafiya, gaskiya, adalci, da hidimar al’umma. Mai Martaba Sarkin Zazzau na kira ga dukkan Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’a don ci gaba da zaman lafiya da wadata a Masarautar Zazzau, Jihar Kaduna, da Kasa baki daya.”

Alhaji Abbas Fatika ya kuma jaddada kira ga iyaye da su kara himma wajen koya wa ‘ya’yansu kyawawan halayen addini da kuma tallafawa shirye-shiryen ilimin Al’Qur’ani a Masarautar.

Haka kuma a Fadar Mai Martaba Sarkin Zazzau, manyan malamai sun gabatar da Jawabi bisa muhimmancin Annabi Muhammad S.A.W ga al’ummar Musulmi. Taron ya kuma samu halartar makarantun Islamiyya, da kungiyoyi, daban-daban.

Mai Martaba Sarkin Zazzau ta bakin Sarkin Fadan Zazzau ya yaba wa masu shirya taron bisa gudanar da shi cikin lumana, kuma ya yi addu’ar Allah Ya karbi addu'o'in da ake yi.

Yada Labarai, na Masarautar Zazzau

With Aishatu Gidado Idris – I'm on a streak! I've made it onto their weekly engagement list 9 weeks in a row. 🎉
25/08/2026

With Aishatu Gidado Idris – I'm on a streak! I've made it onto their weekly engagement list 9 weeks in a row. 🎉

With Sadiq Abubakar Salihu – I'm on a streak! I've made it onto their weekly engagement list 5 weeks in a row. 🎉
25/08/2026

With Sadiq Abubakar Salihu – I'm on a streak! I've made it onto their weekly engagement list 5 weeks in a row. 🎉

Talata, Rabi'ul Awwal 12, 1448AH Tuesday,  August 25, 2026DAGA MASARAUTAR ZAZZAU:-MAI MARTABA SARKIN ZAZZAU YA ZIYARCI F...
25/08/2026

Talata, Rabi'ul Awwal 12, 1448AH
Tuesday, August 25, 2026

DAGA MASARAUTAR ZAZZAU:-

MAI MARTABA SARKIN ZAZZAU YA ZIYARCI FADOJIN ORODJE NA OKPE DA OVIE NA AGBON A JIHAR DELTA*

Rahoto, ABDULLAHI ALIYU KWARBAI

A ci gaba da ziyararsa a Jihar Delta domin ƙarfafa zumunci da hadin kai tsakanin sassan al’ummar Nijeriya, Mai Martaba Sarkin Zazzau kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kaduna, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR, a yau ya kai ziyarar girmamawa ga fadojin sarakuna biyu a jihar.

Mai Martaba Sarkin Zazzau ya fara da kai ziyara zuwa Fadar Orodje na Masarautar nOkpe, Mai Alfarma, Manjo Janar Felix Mujakperuo (Mai Ritaya), CFR, mni.

Daga nan kuma ya kai ziyara zuwa Fadar Ovie na Masarautar Agbon, Mai Alfarma, Mike Omeru, Ogurimerime Ukoro I, CON.

A jawabansa, Mai Sarkin Zazzau ya isar da sakon gaisuwa daga al’ummar Masarautar Zazzau, tare da jaddada muhimmancin hadin kai, girmamawa juna, da hadin gwiwa tsakanin Sarakunan gargajiya a fadin Nijeriya domin samun zaman lafiya da ci gaba.

Cikin 'yan rakiyan Mai Martaba Sarkin Zazzau sun hada da Durbin Zazzau, Alhaji Muhammad Aminu Aliyu Bamalli, da Jarman Zazzau, Alhaji Muktar Shehu Ibrahim, da kuma wasu daga cikin yaran Fadansa.

Sarakunan sun tarbi Mai Martaba Sarkin Zazzau da tawagar sa cikin girmamawa, inda s**a bayyana ziyarar a matsayin wata muhimmiyar mataki na ƙarfafa dangantaka tsakanin al’ummar Arewacin Nijeriya da Kudu.

Yada Labarai, na Masarautar Zazzau

Address

Kwarbai Madarkaci Zaria City
Kaduna

Telephone

+2348031957267

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Yaks Idris Bamalli Zazzau Emirates photographer posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Yaks Idris Bamalli Zazzau Emirates photographer:

Shortcuts

Share

Category