13/08/2026
Allah Sakawa mahaifiya da gidan Aljannah Fiddausee, ka bamu ikon Masu biyayya da dukkannin abun da muke da halinsa anan Duniya da mafificin Duniyar. Bisa tafarkin koyarwar Fiyayyen Hallita. Ameen ya Hayyu ya Qayyum, ya Zuljalalu Wal'ikiram
Darasi: Cibiya wani tabo ne bayan yanke jijiyar cibiya daga jikin mabiyya, wato "placenta" a turance. Wannan tabon yanke cibiya yana wanzuwa tsawon rayuwa kuma wanzuwar tasa yana ɗauke da darasi mai muhimmancin gaske gare mu.
Muhimmin darasin shi ne, cibiya wani tambari ne da aka buga wa kowa domin ya dinga tuna mana cewa akwai wata baiwar Allah wace rayuwarmu ta dogara da rayuwarta kacokan har tsawon watanni tara. Ta cikin cibiyar ne take ba mu ci da sha lokacin da ba mu san kanmu ba.
Allah Ya saka musu da mafificin alheri.
Da zarar ka gama karanta wannan bayani, ina ba da shawarar yi wa mahaifanmu addu'a ta musamman.
© Physiotherapy Hausa