11/09/2022
πππππππππππ
Wani ne yaje wurin walima sai ya zauna layin gaba sai aka
shigo da abinciπ²ππ sai aka fara rabawa daga
baya kafin azo wurin shi abincin ya kareπβΊ; Sai ya
tashi ya koma baya, sai aka shigo da naman kajiππ
sai kuma aka fara rabawa daga gaba kafin azo wurin shi
naman ya kareπππ³; sai ya tashi ya koma tsakiya
haushi ya kule shi, ya kwantar da kansa bisa tebur kawai
sai yaji ance malam bismillah ya d**o kai sai aka miko
mai tsinken sakaceπ tunaninsu harya gamaci hutawa
yake. Sai ya tashi ya sharama mai rabon abincin mari yace
aka gayamaka ni mayene banci abinciba banci namaba sai
itace. ππ.Dan boko
Wani matashi ne dan karya kuma dan boko, ya kammala
karatunsa amma ba aiki; ya yi ta kokarin neman aiki bai samu
ba. Wata rana wani manajan kamfani ya ce ya je ya yi masa
intabiyu, domin daukarsa aiki. Da ya je, ga abin da ya wakana
a tsakaninsu:
Manaja: Mene ne sunanka?
Dan boko: KF.
Manaja: Mene ne KF?
Dan boko: Kabir Faruk.
Manaja: Wane gari kake?
Dan boko: KF.
Manaja: Mene ne KF?
Dan boko: Kwanar Farakwai.
Manaja: Wace unguwa kake?
Dan boko: Ni fa komai KF ne.
Manaja: Mene ne KF?
Dan boko: Kofar Fada.
Manaja: Wace makaranta ka yi?
Dan boko: KF.
Manaja: Me ke nan?
Dan boko: Kwalejin Fasaha.
Manaja: Me ke sanaβarka?
Dan boko: KF.
Manaja: Mene ne KF?
Dan boko: Kota da Fartanya.
Dan boko: To yaya labarin KF?
Manaja: Mene ne KF?
Dan boko Labarin Kokarina Fa?
Manaja: To kai ma KF.
Danboko: Ah! Manaja, mene ne kuma KF? Manaja: Ka Fadi.
Daga Buhari Liman
Mai Danwake