12/27/2025
SHIN KAI NE NA ASALI, KO "KWAFIN" NE KAI ?
Idan ka kalli kanka a madubi, kana ganin mutum daya ne wanda aka haifa shekaru ashirin ko talatin da s**a wuce. Amma yau, ina so in nuna maka cewa wannan tunanin babban kuskure ne. A zahiri, kai ba mutum daya ne tun daga haihuwa zuwa yau ba. Kai wani "labari" ne kawai mai gudana wanda haruffansa suke canzawa kowane lokaci.
1. Jirgin Theseus
A zamanin dā, akwai wani jirgin ruwa na jarumi Theseus. Domin jirgin ya dawwama, duk lokacin da katako daya ya ruɓe, sai a cire shi a sa sabo. Bayan shekaru masu yawa, dukkan katakan jirgin, igiyoyinsa, da kofofinsa an riga an sauya su da sababbi.
Anan ne rikitarwar take: Shin wannan jirgin, wanda babu ko kwayar katako daya na asali a jikinsa, har yanzu shi ne "Jirgin Theseus"?
Idan ka ce Eh, to kana nufin asalin jirgi ba jikinsa ba ne. Idan kuma ka ce A'a, to a wane mataki ne ya daina zama na asalin? Lokacin da aka canja katako na farko, ko na karshe?
2. Kai Ma Jirgin Ruwa Ne (Hujjar Kimiyya)
Wannan ba tatsuniya ba ce kawai; jikinka ma haka yake. Kwayoyin halittarka (Cells) suna mutuwa ana maye gurbinsu a kowane dakika.
Fatarka: Ana canja ta gaba daya kusan kowane mako huɗu.
Jininka: Kwayoyin jini suna mutuwa ana samar da wasu duk bayan kwanaki 120.
Kashinka: Ko kashinka mai tauri, ana canja shi baki daya duk bayan shekaru goma.
Wannan yana nufin cewa kwayoyin halittar da mahaifiyarka ta haife ka da su, ba su ne suke jikinka yanzu ba. Su duka sun rube, sun zama kura, sun bace. Jikinka na yanzu "sabo" ne ful, wanda aka gina shi daga abincin da ka ci a 'yan shekarun nan.
3. Wayar Salula: Misalin Bayanai (Data)
Ka yi tunanin kana da waya, sai ta fashe. Ka siyi sabuwa, ka shigar da "Email" dinka, dukkan hotunanka da bayananka s**a dawo cikin sabuwar wayar. Shin za ka ce wannan wayar "taka ce ta dā"?
A zahiri, sabuwar waya ce mai dauke da tsoffin bayanai. Haka kake: jikinka sabo ne, amma kwakwalwarka tana dauke da "tsohon tunani". Kai ba jikin ba ne; kai wani "Data" ne da yake yawo