11/11/2025
DARASI GA MASU HANKALI
Mahaifiyar wannan yaro matashin Malamin darika Abul Fathi ta rasu jiya, ya sanar da rasuwarta, munanan maganganun da wasu s**ayi akan mutuwarta bai dace ba
Lokacin da Marigayi Sheikh Dr Idris Abdul-Aziz Bauchi ya rasu, wannan yaro Abul Fathi ya fadi munanan kalamai a kan Malam
Sai gashi jiya Allah Ya karbi rayuwar Mahaifiyarsa, irin kalmomin jahilci da wauta da yayi amfani dasu akan rasuwar Malam Idris Abdul-Aziz haka aka dinga yiwa Mahaifiyarsa
Na tabbata yaji zafin kalmomin kamar yadda daliban Malaman Idris da masoyansa s**a ji zafin kalmar da yayi amfani da ita akan rasuwar Malam Idris
To wannan darasi ne, wani lokaci mutum tun a duniya yake fara karban sakamakon munanan aikinsa kafin a isa lahira
Duk sabani da gabar dake tsakaninka da Musulmi idan akace ya kwanta ya mutu, idan ba zaka roka masa gafaran Allah ba to ka rufe bakinka, musamman saboda ita mutuwa wajibi ne akan kowa
Sannan 'yan uwa da muke kan akida daya wadanda s**a fadi kalma marar dadi akan Mahaifiyar Abul Fathi baku kyauta ba, ba tarbiyyan Ahlussunnah bane wannan, idan wawa mahaukacin kare yayi haushi ba'a tanka masa, sannan laifin Abul Fathi bai shafi na Mahaifiyarsa ba
Muna rokon Allah Ya jikan mahaifiyarsa, shi kuma Allah Ya shiryar da shi