Tsalle daya

Tsalle daya in here you find what you need. the swag is for all.

Babbar magana!! Wasu kwararru a jami'ar Bonn da ke Jamus sun gano cewa shan tabar Wiwi na kara inganta lafiyar tsofaffi....
17/01/2026

Babbar magana!! Wasu kwararru a jami'ar Bonn da ke Jamus sun gano cewa shan tabar Wiwi na kara inganta lafiyar tsofaffi.

Tawagar karkashin jagorancin Andras Beilke-Gorzo ta gano cewar zukar tabar Wiwi ka iya takaita saurin tsufan kwakwalwa idan har wadanda s**a manyanta suna sha

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce, gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen ci gaba da bujiro da sabbin matakai...
01/01/2026

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce, gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen ci gaba da bujiro da sabbin matakai da tsare-tsaren da zasu bunkasa tattalin arzikin kasar.

TSALLE DAYA°

Da dumi dumi ta.Kungiyar kwallon kafa ta birtania, (chelsea) ta sallami managan ta Enzo maresca.
01/01/2026

Da dumi dumi ta.

Kungiyar kwallon kafa ta birtania, (chelsea) ta sallami managan ta Enzo maresca.

NAWA NE HARAJIN? Hukumar tattara harajin ta tarayya wato FIRS, wadda yanzu ta koma Nigeria Revenue Service wato NRS, a k...
01/01/2026

NAWA NE HARAJIN?

Hukumar tattara harajin ta tarayya wato FIRS, wadda yanzu ta koma Nigeria Revenue Service wato NRS, a kundin da ta fitar ta nuna cewa kasancewarku ƴan Najeriya ba shi ne zai sa ku biya harajin ba illa dai yawan samun da kuke yi, inda ta saka sharaɗin da sai mutum ya kai zai fara biyan haraji.

Babu haraji a kan N800,000 ta farko
N2,200,000 za a biya kaso 15 na kuɗin
N9,000,000 za a biya kaso 18 na kuɗin
N13,000,000 za a biya kaso 21 na kuɗin
N25,000,000 za a biya kaso 23 na kuɗin
N50,000,000 za a biya kaso 25 na kudin

JERIN MUTANE DA ABUBUWAN DA AKA DAUKE WA HARAJI.

Bisa kundin hukumar tattara harajin ta Najeriya, an ɗauke harajin daga kan wasu kuɗade da mutane k**ar haka:

Mutumin da ke samun kuɗi daidai da albashin ma'aikacin Najeriya mafi ƙanƙanta na N72,000, a wata.
Mutumin da samunsa a shekara bai wuce N1,200,000 ba.
Kyauta (babu haraji a kyauta).
Kuɗin da mutum ke tarawa na fansho.
Kuɗin fansho da garatuti.
Kuɗin insorar lafiya.
Asusun lamunin gidaje.
Riba a kan kuɗaɗen rance na mutumin da ke cikin gida yake son ya malleke shi.
Kuɗaɗen insora.
Kuɗin sallamar ma'aikaci daga aiki da ba su wuce N50,000,000 ba.
Kuɗin da aka sayar da gidan da aka ma'aikaci ya mallaka bayan shekaru yana zaune a ciki.
Kuɗin da mutum ya sayar da wata kadara da bai wuce N5,000,000 ba.
Sayar da motoci na ƙashin kai da ba su wuce biyu a shekara ba.
Riba a kan hannun jarin da ba ta kai N150,000,000 a shekara ko kuma N10,000,000.
Kuɗaɗen jinƙai da na ƙungiyoyin addini (waɗanda ba don riba aka kafa su ba)
Ƙananan masana'antu da uwar kuɗin jarinsu ba ta wuce N100,000,000 ba ko kuma gabaɗaya jarin bai wuce N250,000,000.
Ƙananan ƴan kasuwa da suke tasawa

A ranar 1 ga watan Janairun 2026 ne ake sa ran sabuwar dokar haraji ta Najeriya za ta fara aiki wadda shugaba Bola Ahmed...
01/01/2026

A ranar 1 ga watan Janairun 2026 ne ake sa ran sabuwar dokar haraji ta Najeriya za ta fara aiki wadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya saka wa hannu domin amincewa ta zama doka.

An dai ta tunanin cewa za a dakatar da fara aiwatar da harajin kafin sabuwar shekara sak**akon zarge-zargen cushe da aka yi wa dokar ta haraji, wadda aka ce ta bambanta da asalin wadda majalisar dokoki ƙasar ta amince da ita.

A ranar 30 ga watan Disambar 2025 ne shugaba Tinubu ya sanar da cewa babu buƙatar dakatar da fara aiwatar da harajin domin hakan zai katse wa Najeriya burinta na samar da cigaban da ake buƙata.

Sai dai ya ce yana sane da irin zarge-zargen da ake yi dangane da cushe a dokar kuma yana aiki da majalisar dokokin ƙasar wajen samar da mafita.

Yanzu dai abin da al'ummar Najeriyar ke son sani shi ne ta yaya wannan haraji zai shafe su daga ranar 1 ga watan Janirun sabuwar shekarar 2026? BBC ta yi nazarin dokar harajin ga kuma bayanan da ta tattara.

Wata ‘yar kasuwa a Lapai, Jihar Neja, Hajiya Aisha Isah Adamu, ta mayar da Naira miliyan 330 da aka tura mata a asusun b...
31/12/2025

Wata ‘yar kasuwa a Lapai, Jihar Neja, Hajiya Aisha Isah Adamu, ta mayar da Naira miliyan 330 da aka tura mata a asusun bankinta bisa kuskure. Ta gano kuɗin ne a asusun ta na First Bank a ranar 29 ga Disamba, 2025, yayin da take duba matsalar cire mata kuɗi ba tare da izini ba.

Bayan ta tabbatar da cewa kuɗin ba nata ba ne, ta kai rahoto ga banki, inda aka gano kuskuren tsarin banki ne, sannan aka mayar da kuɗin. Hajiya Aisha ta ce ta yi hakan ne saboda mutunci da kuma kare makomar ’ya’yanta. Lamarin ya ja hankalin jama’a, inda da dama s**a yaba mata bisa gaskiya da amana.

Kungiyar Shinkafan Nupe ta mayar da martani ga Niger Foods, ta ce maganganunsu “raunana ne kuma marasa gaskiya”Kungiyar ...
10/11/2025

Kungiyar Shinkafan Nupe ta mayar da martani ga Niger Foods, ta ce maganganunsu “raunana ne kuma marasa gaskiya”

Kungiyar Shinkafan Nupe Agro Allied Services ta mayar da martani mai zafi ga kamfanin Niger Foods, tana bayyana sanarwar da kamfanin ya fitar a baya a matsayin “raunana, marar ma’ana, cike da karya da rashin gaskiya.”

A cewar kungiyar, kamfanin Niger Foods ya nuna rashin kwarewa da cin hanci, tare da jaddada cewa batun dake tsakaninsu yanzu yana gaban kotu. Shinkafan Nupe ta bayyana cikakken yarda da tsarin shari’a, tana mai cewa suna da tabbacin adalci daga kotu.

Kungiyar ta kuma roki jama’a da su bi diddigin shari’ar domin su gane gaskiyar lamari, tare da neman a saki shugabansu, Malam Idris Usman Makanta, wanda ake zargin yana tsare duk da cewa akwai umarnin kotu da ke ba da damar a sake shi.

Bugu da ƙari, Shinkafan Nupe ta kalubalanci Niger Foods da ta fito fili ta bayyana takardun bayanan duk wani abin da ta ce ta karɓo ko ta dawo da shi, domin tabbatar da gaskiya da bayyana adalci a cikin rikicin da ke gudana.

Mutum Ya Rasa Ransa Bayan Zargin Satar Babur a GbokoWani mutum da ake zargi da satar babur ya rasa ransa bayan da wasu f...
09/11/2025

Mutum Ya Rasa Ransa Bayan Zargin Satar Babur a Gboko

Wani mutum da ake zargi da satar babur ya rasa ransa bayan da wasu fusatattun matasa s**a banka masa wuta a unguwar Abagu da safiyar yau, Lahadi.

Rahotanni sun ce mutumin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an cafke shi ne bayan da aka yi zargin ya saci babur a yankin. Sai dai kafin jami’an tsaro su isa wajen, wasu daga cikin jama’ar da s**a taru sun kai masa hari s**a kuma kona shi har lahira.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Jama’a sun k**a shi da babur da ake zargi ya sata. Maimakon su kai shi ofishin ‘yan sanda, sai s**a dauki doka a hannunsu.”

Jami’an ‘yan sanda na jihar Benue ba su bayar da cikakken bayani ba a halin yanzu, amma wata majiya ta tabbatar cewa an fara bincike kan lamarin.

Masana harkokin tsaro da kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun sha yin kira ga jama’a da su guji daukar doka a hannunsu, suna mai jaddada cewa irin wannan mataki ba kawai laifi ba ne, yana kuma kawo barazana ga zaman lafiya da adalci.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa ya ɗauki matakain sauya hafsohin tsaron ƙasar, yana mai gode w...
25/10/2025

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa ya ɗauki matakain sauya hafsohin tsaron ƙasar, yana mai gode wa tsofaffin manyan jami'an tsaron da ya sauke.

Wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ya ce ya ɗauki matakin ne saboda "ƙyautata tsaron ƙasa"

"Na amince da sauya shugabancin rundunar tsaro domin ƙarfafa tsarin tsaron Najeriya," in ji shi.

"Ina gode wa Janar Christopher Musa da sauran hafsoshin tsaron da s**a gabata saboda hidima da sadaukarwar da s**a yi, kuma ina neman sababbin shugabannin da su kyautata ƙwarewar aiki, da ankararwa, da haɗin kai a tsakanin sojojinmu."

Sauyin shugabannin rundunar sojin na zuwa ne a lokaci da ake ci gaba da raɗe-raɗi game da shirin juyin mulki da aka ce wasu sojoji sun tsara, zargin da rundunar sojin ta musanta.

Ɗan shugaban Najeriya, Seyi Tinubu ya faɗi hakan ne yayin wani taro da matasa a jihar Adamawa da gidauniyarsa ta shirya....
20/03/2025

Ɗan shugaban Najeriya, Seyi Tinubu ya faɗi hakan ne yayin wani taro da matasa a jihar Adamawa da gidauniyarsa ta shirya.

A cikin kwanakin nan Seyi yana ziyarar jihohin arewa inda ya ke yin buɗe-baki tare da al’umma.

18/03/2025

Baki shike yanke wuya, akoda yaushe ka rika kula da harshen ka

Address

Minna
Minna
920101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tsalle daya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category