09/06/2026
BA RADDI BANE......
Tsokaci ne akan wani bidiyo da naga sirrin Fatahi Mawaƙi daga Dariqar TIJJANAWA yana sakin harshe akan Imam Mahdi (AF)— Ba da nufin ya san shi ba— tausayi ya bani, irin tausayi sosai ɗin nan jama'a. Wato sai yanzu na sake dawo hayyacina na tuna cewa lalle fa mutanen mu basu san Ahl-bayt (As) ba.
Kar ka ja da nisa, Imam Husayn (As), ɗan Nana Faɗima (S) ƴar Manzon Allah Annabi Muhammad (S), wacce aka sauke Surar Kausar Saboda ita, kaga kenan tsakanin Imam Husayn da Manzon Allah (S) mutun ɗaya ne wato Nana Faɗima (SA), wacce Sirrin Fatahi ke neman ceton ta, wacce yake cewa KAYAN ALLAH NATA NE, NA ANNABI MA nata ne.
A Shekara ta 61 bayan Hijira, Musulmi s**ai gangami ƙarƙashin Yazidu ɗan Mu'awiya, a cikin masu gangamin daga ƴaƴan Sahabbai sai wadda s**a rayu tare da Sahabbai, s**a kewaye ɗan Manzon Allah ta hanun Nana Faɗima wato Imam Husayn a dajin Karbala s**a kashe shi, kufa duba ba wata rata mai yawa aka samu da Wafatin Annabi (S) ba s**ai wannan aika aikar.
Amma da Imam Husayn ya tsaya yana musu bayani a filin yaƙin kafin su afka masa, wasu sai s**a fashe da kuka saboda su basu ma san wa s**a zo yaƙa ba, wato basu san wadda ya kawo su filin yaƙin ba (Yazidu), basu san wa suke yaƙa ba (Imam Husayn), a wannan wurin Kwamanda guda daga rundunar Yazidu Wato Hurr bn Rayyan ya karɓi Musulunci irin na gidan Ahl-Muhammad yabi Imam Husayn, karfa kuce wadda s**a zo kashe shi Kiristoci ne, A'a, Musulmi ne ƴaƴan Sahabbai da Jikokin su kamar yadda na kawo a baya.
To idan Jahilcin wannan Al'umma ya kai ta kashe ɗan Manzon Allah (S) kuma a cikin Musuluncin da Annabin sa bai daɗe da Wafati ba, mai kuke tsammani daga wannan Al'umar da tai Shekaru sama da 1,400 nisan ta da Manzon Allah (S) don tayi sukuwa akan Alfarmar Imam Mahdi (AF)?. Kana Sharifi, Mawaƙin gidan Annabta, amma ba kasan zuriyar Annabin da kake waƙewa ba, akwai abin tausayi irin wannan?. Kai Jama'a! INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN.
Ba shakka akwai haƙƙi a wuyan dukkan wadda ya fahimci