18/05/2026
A Shekarar 1992 Mai girma Engrn Dr Rabi'u Musa Kwankwaso yana matsayin Deputy speaker a majalisar Nigeria ya dako wani matashi ɗan shekara 29 wanda yaronsane a ma'aikatar ruwa a shekarun 1980s, ya nadashi a matsayin P.A dinsa
A Shekarar 1999 bayan KWANKWASO ya cigaba da gwagwarmayar siyasa daga 1992, shikuma wancan matashi yakoma aikin gidan ruwa , katsam kwankwaso yaci gwamnan Kano , haka ya kara nemo wannan matashi yaqara nadashi PA ɗinsa yazama PA na gwamna
A shekarar 2003 bayan Rashin nasarar zaɓe da kwankwaso yayi , sai gwammanatin tarayya ta nadashi babban ministan tsaron Nigeria , kwankwaso bai bar matashin nanba haka yaqara ɗaukeshi yayi Abuja dashi ya naɗashi S.A ɗinsa.
A Shekarar 2007 bayan Kwankwaso yabar ministan tsaro , Obasanjo yasake nadashi a matsayin Special Envoy to Somalia and dafur, Kwankwaso haka yaqara tafiya da wannan matashi a matsayin mai taimaka masa na musamman kuma na hannun damansa
A Shekarar 2009 a hukumar NDDC Yar aduwa ya nada kwankwaso wakilin Northwest, kwankwaso yaqara tafiya da matashin nan a matsayin na hannun damarsa, a dai wannan shekarar ta 2009 Kwankwaso ya nema masa federal appointment akayi kuma Sa'a marigayi Yar aduwa ya nadashi a matsayin chairman, Governing Board of the National Institute for Educational Planning and Administration (NIEPA), Ondo State.
A Shekarar 2011 Kwankwaso yadawo yazama gwamnan Kano a karo na biyu, haka ya sake dako matashin nan ya dankara masa kujerar kwamishina a katotuwar ma'aikata
A shekarar 2019 , bayan Kwankwaso yagama gwamna a 2015 sai wannan matashi ya ɗanja baya a harkar siyasa har zuwa shekarar 2018 inda kwankwaso ya ɗaukoshi yace shizai takarar gwamna a PDP wannan taja kwankwaso ya rasa yara da aminai sbd ganin kamar ya dako wanda bai isaba ko bai kaisuba, aka shiga zaɓe akaci zaɓe, akace Inconclusive aka sake ganduje yakoma kujerarsa
A Shekarar 2023, kwankwaso yasake ɗako wannan matashi yace shine dai zaiyi takara, rashin tsayayyar structure dazata bashi damar tsaida wannan matashi tasa kwankwaso yabar PDP ya dako wata qaramar Jam'iyya wanda ba kowa ya santaba mai suna NNPP yakoma ita tare da magoya bayansa da wannan matashi yaqara tabbatar masa da takara, aka shiga zaɓe akaci zaɓe wannan matashi yazama Gwamnan Kano
Tarihin yanada daɗin ji saidai kuma kash bayan wannan matashi yazama gwamna da shekara 2 kacal, tarihin saiya zama mara daɗi daga qarshen shekarar 2025 zuwa cikin shekarar 2026, zanci gaba.....
Suleiman Lawan Gogori 🖋️
Kwankwasiyya loyalist 🔴
18/5/2026