Voice of katsina

Voice of katsina VoiceofKatsina a dynamic media forum
Truth, Transparency, advocacy & progress(T-TAP)

Make it easy for you...

𝗡𝗔𝗝𝗘𝗥𝗜𝗬𝗔 𝟮𝟬𝟮𝟳: Yakin Neman Zaɓe Zai Fara Gobe LarabaA hukumance, gobe Laraba, 19 ga Agusta 2026, ne za a fara yakin nema...
18/08/2026

𝗡𝗔𝗝𝗘𝗥𝗜𝗬𝗔 𝟮𝟬𝟮𝟳: Yakin Neman Zaɓe Zai Fara Gobe Laraba

A hukumance, gobe Laraba, 19 ga Agusta 2026, ne za a fara yakin neman zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Tarayya na shekarar 2027.

Yayin da yakin neman zaɓen ke shirin farawa, ana sa ran za a ga sauye-sauyen jam’iyyu, sabbin ƙawance, cin amanar siyasa da kuma sabbin alkawura daga ’yan siyasa.

Tsoffin jawabai da bidiyoyi za su iya sake bayyana, tsoffin abokan hamayya su koma ƙawaye.

Duk da haka, muna fatan zaɓen 2027 zai kasance na lumana, gaskiya da adalci, kuma muna yi wa dukkan ’yan takara fatan alheri ba tare da la’akari da jam’iyyar da suke wakilta ba.

IPAC: Sakamakon Zaben Osun Ya Tabbatar da Aniyar Al’umma Ta Ci Gaba Da Rike AdelekeOsogbo — Kungiyar Inter-Party Advisor...
17/08/2026

IPAC: Sakamakon Zaben Osun Ya Tabbatar da Aniyar Al’umma Ta Ci Gaba Da Rike Adeleke

Osogbo — Kungiyar Inter-Party Advisory Council (IPAC) reshen Jihar Osun ta taya Gwamnan jihar, Sanata Ademola Adeleke, murnar sake lashe zaben gwamnan jihar, tana mai cewa sakamakon zaben ya nuna aniyar al’ummar jihar na ci gaba da rike shi a matsayin gwamna na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

A cikin wata sanarwa da Shugaban IPAC na jihar, Tosin Odeyemi, ya sanya wa hannu, kungiyar ta yaba wa al’ummar Osun bisa yadda s**a fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri’unsu cikin lumana.

IPAC ta kuma yabawa INEC, jami’an tsaro, kafafen yada labarai, kungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki bisa gudunmawar da s**a bayar wajen ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Kungiyar ta ce sakamakon zaben ya nuna amincewar al’ummar jihar da ayyukan da Adeleke ya gudanar a zangon farko, tare da sabunta musu kwarin gwiwa na ci gaba da jagorancinsa.

IPAC ta bukaci gwamnan da ya tafiyar da mulkinsa na biyu ba tare da nuna banbancin jam’iyya ba, tare da bai wa ‘yan adawa, kwararru, mata, matasa, masu nakasa da hukumomin gargajiya damar bayar da gudunmawarsu wajen ci gaban jihar.

Haka kuma, kungiyar ta bukaci gwamnatin Adeleke da ta tabbatar da cewa rabon mukamai da ayyukan raya kasa ya shafi dukkanin yankunan Sanatoci uku da kananan hukumomi 30 na jihar, ciki har da Area Office.

Ta ce babu wata al’umma da ya kamata ta ji an bar ta a baya, domin samar da hadin kai da ci gaba mai dorewa.

IPAC ta kuma yi kira ga gwamnan da kada sake lashe zabe ya sa a rage kaimi wajen gudanar da ayyukan gwamnati, tana mai cewa wannan zangon na biyu dama ce ta kammala ayyukan da aka fara tare da kirkirar sababbin ayyukan da za su amfani al’umma na dogon lokaci.

Kungiyar ta ce al’ummar Osun na sa ran samun karin ingantaccen aiki a bangarorin ilimi, lafiya, noma, samar da ababen more rayuwa, samar da ayyukan yi ga matasa da walwalar jama’a.

IPAC ta bayyana shirinta na ci gaba da taka rawa a matsayin abokiyar adawa mai gina kasa, inda ta ce za ta rika s**ar manufofin gwamnati ne bisa batun da ya shafi al’umma, tare da mara wa duk wata manufa da ta dace da muradun mutanen Osun baya.

Daga: Voice of Katsina

INEC Ta Bayyana Adeleke a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaɓen OsunHukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Gwamna...
16/08/2026

INEC Ta Bayyana Adeleke a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaɓen Osun

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Gwamna Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Osun na 2026.

Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord, ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar, inda ya samu ƙuri’u 511,067.

Bayan bayyana sakamakon, fitaccen mawakin Najeriya Davido, wanda ke da alaƙa da Adeleke, ya bayyana farin cikinsa tare da taya shi murna kan nasarar.

Davido Ya Ce Adeleke Na Kan Gaba, Ya Caccaki APCFitaccen mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, y...
15/08/2026

Davido Ya Ce Adeleke Na Kan Gaba, Ya Caccaki APC

Fitaccen mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya bayyana cewa gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, wanda kuma kawunsa ne, na kan gaba a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar.

Davido, wanda ya fito fili ya nuna goyon bayansa ga Adeleke, ya bayyana hakan ne a wasu sakonnin da ya wallafa a kafafen sada zumunta yayin da ake ci gaba da kirga kuri'u a fadin jihar.

Mawakin ya kuma yi ikirarin cewa jam'iyyar APC ta sha kaye a rumfar tsohon gwamnan Osun, Bisi Akande.

“Kungiyarsu ta tarwatse! Baba Akande ya rasa rumfarsa. Gwamna Adeleke na kan hanyar samun nasara. Kunya APC, Osun ba Edo ba ce,” in ji Davido.

Davido ya kuma bukaci al’ummar Osun da su kasance cikin taka-tsantsan, tare da kira ga jami’an tsaro da kada su janye daga wuraren kada kuri'a har sai an kammala aikin zaben.

Ya ce: “Muna samun nasara. Bai kamata jami’an tsaro su janye daga rumfunan zabe ba.”

A halin yanzu, hukumar INEC na ci gaba da tattara da loda sakamakon zaben, yayin da har yanzu ba a ayyana wanda ya lashe zaben a hukumance ba.

Osun 2026: Adeleke Ya Fara Jan Ragama Yayin da Ake Ƙidaya Ƙuri’uGwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya fara jan ...
15/08/2026

Osun 2026: Adeleke Ya Fara Jan Ragama Yayin da Ake Ƙidaya Ƙuri’u

Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya fara jan ragama a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar yau Asabar, yayin da ake ci gaba da ƙidaya da tattara sakamakon zaɓe.

Rahotannin farko daga rumfunan zaɓe da aka fara tattara sakamakonsu sun nuna cewa Adeleke, wanda ke neman wa’adin mulki na biyu a ƙarƙashin Accord Party, na kan gaba a wasu daga cikin sakamakon da aka fara samu, yayin da babban abokin hamayyarsa na APC, Bola Oyebamiji, ke fafatawa da shi sosai.

A halin yanzu, hukumar INEC na ci gaba da tattara sakamakon daga rumfunan zaɓe da kuma ɗora sakamakon da aka tantance a dandalin IReV. Rahotanni sun nuna cewa ɗaruruwan sakamakon rumfunan zaɓe sun riga sun bayyana a dandalin, yayin da ake jiran sauran sakamakon.

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta sanar da kudin aikin Hajjin shekarar 2027, tare da bayyana wa maniyy...
15/08/2026

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta sanar da kudin aikin Hajjin shekarar 2027, tare da bayyana wa maniyyata wa’adin da aka sanya na kammala biyan kuɗaɗen Hajjin.

A cewar sanarwar, an kayyade kuɗin Hajjin ne bisa yankunan tashin maniyyata, tare da la’akari da farashin canjin kuɗi da kuma kuɗaɗen hidimomin da ake bayarwa a Saudiyya.

Ga kudin Hajjin da aka amince da su:

* Yankin Maiduguri/Yola: ₦7,560,822
* Yankin Arewa: ₦7,672,822
* Yankin Kudu: ₦7,882,822

Hukumar ta ce maniyyatan da s**a riga s**a biya ₦5,000,000 za su biya ragowar kuɗin domin kammala rajistarsu.

Sabbin maniyyata kuma an shawarce su da su biya kuɗaɗen ta hannun Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohinsu ko wasu hanyoyin ajiyar kuɗin Hajji da aka amince da su.

NAHCON ta kuma sanya 26 ga Satumba 2026 a matsayin ranar ƙarshe kuma ta ƙarshe da za a kammala ɗora bayanan biometric na maniyyata a tsarin dijital na Nusuk-Masar.

Haka kuma, jihohi za su kammala tura dukkan kuɗaɗen aikin Hajjin 2027 zuwa 2 ga Disamba 2026.

Hukumar ta jaddada cewa ba za a ƙara wa’adin ba, saboda tsarin daidaita bayanan maniyyata da kuma rabon kujerun jirgi ya dogara ne da kammala biyan kuɗaɗen a kan lokaci.

NAHCON ta gargadi cewa rashin cika waɗannan wa’adin na iya jawo rasa guraben Hajjin da aka ware wa jihohi.

Dan takarar kujerar Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen 2027, Hon. ...
14/08/2026

Dan takarar kujerar Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen 2027, Hon. (Barr.) Abba Dahiru Mangal, ya kai ziyara gidan gyaran hali na Katsina, inda ya biya bashin wasu mutane da aka tsare sakamakon rashin iya biyan basuss**ansu.

A yayin ziyarar da ya kai ranar 13 ga Agusta 2026, Hon. Abba Dahiru Mangal ya nuna tausayi da jinƙai ga wasu daga cikin waɗanda ake tsare da su, inda ya biya musu basuss**an da s**a jawo aka tsare su.

Bayan biyan bashin, an saki mutanen domin su koma cikin iyalansu, lamarin da ya ba su damar sake komawa cikin al’umma bayan tsawon lokacin da s**a shafe a gidan gyaran halin.

Baya ga biyan bashin, Hon. Mangal ya kuma ƙara tallafa wa waɗanda aka saki domin su samu abin dogaro da kai, ta hanyar fara wata sana’a da za ta taimaka musu wajen kula da kansu da iyalansu.

Wannan mataki ya jawo yabo daga masu ganin cewa taimaka wa waɗanda s**a shiga cikin matsalar bashi, musamman waɗanda s**a rasa hanyar biyan bashin da ake binsu, na daga cikin ayyukan jinƙai da ke taimaka wa al’umma.

Abin da Hon. Abba Dahiru Mangal ya yi ya kuma kasance wani misali na yadda taimakon ɗan Adam zai iya sauya rayuwar iyali, musamman idan aka bai wa wanda aka saki damar sake tsayawa da ƙafafunsa ta hanyar samun sana’ar dogaro da kai.

Haka kuma, wannan lamari ya sake buɗe tattaunawa kan muhimmancin tallafa wa mutane masu fuskantar matsalolin tattalin arziki, domin su samu damar komawa cikin al’umma ba tare da sake fadawa cikin irin matsalar da ta kai su gidan gyaran hali ba.

Allah Ya saka masa da alheri, Ya kuma sanya wannan taimako ya zama sanadin sauƙi da ingantacciyar rayuwa ga waɗanda s**a amfana.

DAGA ₦10,220 ZUWA MILIYAN ₦17.8: Me Ya Jawo Sauyin Darajar Naira Cikin Shekaru 48?A shekarar 1978, dala $13,100 ta yi da...
13/08/2026

DAGA ₦10,220 ZUWA MILIYAN ₦17.8: Me Ya Jawo Sauyin Darajar Naira Cikin Shekaru 48?

A shekarar 1978, dala $13,100 ta yi daidai da kusan ₦10,220, lamarin da ke nufin cewa a lokacin $1 ya kai kusan ₦0.78 kacal.

Amma yau, bayan kusan shekaru 48, darajar ta sauya matuƙa. A farashin musayar hukuma na yanzu, $1 yana kusan ₦1,360, wanda ke nufin cewa $13,100 zai kai kusan ₦17.8 miliyan a yau.

Wannan gagarumin sauyin ya haifar da muhawara tsakanin ’yan Najeriya, musamman kan yadda Naira ta samu rauni a cikin shekaru da kuma abubuwan da s**a haddasa hakan.

Me ya sa Naira ta samu wannan gagarumin sauyi daga kusan ₦0.78 kan Dollar a 1978 zuwa sama da ₦1,300 a yau? Kuma me ya kamata Najeriya ta yi domin dawo da ƙarfin tattalin arzikinta?

Me kuke ganin ya kawo wannan sauyi cikin sauri?

Labari cikin hotuna yanda GM Usman Rabiu Mahuta (Talban Ɗandume) ya shirya gasar wasa ƙwaƙwalwa ga ɗaliban makarantu dab...
12/08/2026

Labari cikin hotuna yanda GM Usman Rabiu Mahuta (Talban Ɗandume) ya shirya gasar wasa ƙwaƙwalwa ga ɗaliban makarantu daban-daban da s**a fito daga Ƙaramar Hukumar Ɗandume, inda aka karrama waɗanda s**a yi fice tare da raba kyaututtuka domin ƙarfafa gwiwar matasa wajen neman ilimi.

Hatsari Ya Rutsa da Motar Ma’aikatan Hukumar Zakka da Waƙafi ta Katsina a Hanyar Zuwa SokotoMa’aikatan Hukumar Zakka da ...
12/08/2026

Hatsari Ya Rutsa da Motar Ma’aikatan Hukumar Zakka da Waƙafi ta Katsina a Hanyar Zuwa Sokoto

Ma’aikatan Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Katsina sun gamu da hatsarin mota a tsakanin Yankara da Tsafe a Jihar Zamfara, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Jihar Sokoto domin halartar taron Bankin Raya Musulunci na Duniya (IsDB).

Sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Malam Husain Kabir Yar’adua, ya fitar ta ce mutum ɗaya daga cikin ma’aikatan ya samu karaya, yayin da sauran s**a samu raunuka daban-daban.

An dawo da ma’aikatan zuwa Katsina, inda suke samun kulawar likitoci.

Hukumar ta roƙi al’ummar Musulmi da sauran jama’a da su sanya ma’aikatan cikin addu’o’insu domin Allah Ya ba su lafiya da sauƙin murmurewa.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Voice of katsina posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share