19/02/2026
DAY 002
DAGA OFFISHIN SAKATAREN JAM'IYYAR APC NA JIHAR KANO
JAGORA ALH. IBRAHIM ZAKARI SARINA
Jagora Alh Ibrahim Zakari Sarina
🌙 FADAKARWA KAN RUKO DA IBADA A WATAN RAMADAN
Ya ku ‘yan uwa Musulmi, a wannan rana ta biyu na watan Ramadan, muna kara jaddada muhimmancin riko da ibada, tsarkake niyya, da dagewa wajen aikata alheri.
Allah MaÉ—aukakin Sarki yana cewa a cikin
Al-Qur’ani:
"Ya ku wadanda s**a yi imani! An wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta shi ga wadanda s**a gabace ku domin ku samu taqawa."
(Suratul Baqarah: 183)
Wannan aya tana nuna mana cewa manufar azumi ita ce samun taqawa, wato tsoron Allah da kiyaye dokokinsa a fili da boye.
Haka kuma, Manzon Allah ï·º ya ce:
"Duk wanda ya azumci Ramadan da imani da neman lada, an gafarta masa zunubansa da s**a gabata."
(Bukhari da Muslim s**a ruwaito)
Wannan hadisi yana karfafa mana guiwa da mu dage wajen:
Yin sallah akan lokaci
Karatun Al-Qur’ani
Yawaita istigfari
Ciyar da mabukata
Kyautata mu’amala da jama’a
Mu tuna cewa Ramadan wata ne na gyaran zuciya, yafiya da rahama.
Kada mu bari ranaku su wuce ba tare da cin gajiyar falalar wannan wata mai albarka ba.
Allah Ya ba mu ikon kammala azuminmu lafiya, Ya karbi ibadunmu, Ya sa mu cikin bayinsa na gari.
Amin Ya Rabbal Alamin.
Bashir Hamisu Danbaba
Jagora Alh Ibrahim Zakari Sarina