Da'awatussunnah

Da'awatussunnah Musulunci shine addinin mu 💯
Izzalah Itace aQidarmu
Sunnah Itace Ginshikin Mu
Qur'ani Da Hadith sune Hujjarmu.❤️❤️

*TAKEN MU A YAU: YAU DA GOBE SAI ALLAH ☝️*_Ya dan uwa, Ya 'yar uwa..._Duk abin da kake gani a yau, ba shi ne karshen lab...
12/08/2026

*TAKEN MU A YAU: YAU DA GOBE SAI ALLAH ☝️*

_Ya dan uwa, Ya 'yar uwa..._

Duk abin da kake gani a yau, ba shi ne karshen labarin ka ba.

Yau kana cikin kunci? Gobe Allah zai iya sanya ka cikin yalwa.
Yau kana cikin rashin lafiya? Gobe Allah zai iya baka lafiya cikakkiya.
Yau babu kowa tare da kai? Gobe Allah zai iya kawo maka masoya na kwarai.

*Shin ka manta?*

Fir'auna yana da mulki yau, gobe ya nutse a ruwa.
Annabi Yusuf (AS) yana cikin rijiya yau, gobe ya zama sarki a Masar.

Haka rayuwa take. *Yau da Gobe duk na Allah ne.*

*Nasiha Zalla gare mu:*

*1. Kada ka raina kowa* saboda halin da yake ciki a yau. Wanda ka raina yau, gobe kana iya bukatar taimakon sa.

*2. Kada ka yanke kauna* saboda abin da ya same ka a yau. Kofar Allah ba ta rufe wa.

*3. Kada ka yi girman kai* da abin da Allah Ya baka a yau. Dukiya, kyau, ilimi, mukami - duk aro ne, gobe Allah zai iya karba.

Mu kyautata ayyukan mu na YAU, domin mu samu kyakykyawar GOBE a wajen Allah.

Allah Ka gyara mana yau din mu da goben mu, Ka bamu kyakkyawan karshe.

Amin.

_NASIHA ZALLA ✍️_

🌤️🤍 ADDU’AR MU A YAU — YA ALLAH KA KARƁI BUKATUN DA KE ZUCIYARMU.🤲 Ya Allah…Mun wayi gari a wannan safiyar Litinin…da zu...
11/08/2026

🌤️🤍 ADDU’AR MU A YAU — YA ALLAH KA KARƁI BUKATUN DA KE ZUCIYARMU.

🤲 Ya Allah…
Mun wayi gari a wannan safiyar Litinin…
da zuciya mai rauni…
amma da bege mai girma gare Ka.

Domin mun san cewa
ko duniya ta juya mana baya…
Kai ba Ka taɓa barin bawanka ba.

🤲 Ya Allah…
Akwai addu’o’in da s**a daɗe a bakinmu…
akwai buri da muka daɗe muna jira…
akwai hawaye da muka ɓoye saboda mutane ba su gani.

Ya Allah…
Ka ji kukan zuciyarmu kafin bakinmu ya furta shi.

🤲 Ya Allah…
Ka sa wannan Litinin ta zama farkon alheri a rayuwarmu…
Ka sauya mana abubuwan da s**a dame mu zuwa farin ciki…
Ka cire mana ƙunci da damuwar da ta hana mana sakat.

🤲 Ya Allah…
Idan muna tafiya a hanyar da ba ta da alheri…
Ka dawo da mu gare Ka cikin rahama.

Idan zuciyarmu ta fara mantawa da Kai…
Ka tashe mu kafin mu nutse cikin gafala.

🤲 Ya Allah…
Ka ba mu ikon cin halal…
Ka tsare mu daga wulaƙanci da buƙatar mutane…
Ka sanya albarka a cikin abin da Ka ba mu.

Ka sa mu kasance masu godiya ko da kaɗan ne.

🤲 Ya Allah…
Ka tsare mu daga bakin duniya…
daga abokan da ba su son alherinmu…
daga zuciyar da take cike da hassada da ƙiyayya.

Ka sa mu rayu cikin tsaro da kwanciyar hankali.

🤲 Ya Allah…
Muna roƙonKa lafiya a jiki…
natsuwa a zuciya…
albarka a rayuwa…
da kyakkyawan ƙarshe lokacin da rayuwarmu zata ƙare.

🤲 Ya Allah…
Duk wanda yake karanta wannan addu’a yanzu…
Ka ba shi amsar addu’ar da ya daɗe yana jira…
Ka sanya masa sauƙi daga inda bai zata ba…
Ka cika zuciyarsa da farin ciki da rahama.

🤲 Ya Allah…
Duk wanda ya yaɗa wannan addu’a…
Ka sa rayuwarsa ta zama mai albarka…
Ka gafarta masa da iyayensa…
Ka haɗa su da Annabi Muhammad ﷺ a Aljannah.

🤲 Ameen Ya Rabbal ‘Alameen.

Idan wannan addu’a ta shiga zuciyarka…
rubuta Ameen 🤲
kuma ka tura wa wani…
domin wata zuciya tana jiran sauƙi daga Allah a yau.

Addinu Annasiha

MUJI TSORON ALLAH A DUK INDA MUKE, MU DAINA YAUDARAR KANMU!A kullum mutuwa ta sauka a cikinmu ba zato ba tsammani sai ka...
10/08/2026

MUJI TSORON ALLAH A DUK INDA MUKE, MU DAINA YAUDARAR KANMU!

A kullum mutuwa ta sauka a cikinmu ba zato ba tsammani sai ka aa hankulan mutane na tashi na 'yan wasu mintuna, mutane da dama zasu ɗaura a shafin su "Innalillahi wa'inna ilaihiraj'un"!
Amma abin mamaki da takaici babu abin da ya canza daga cikin munanan ɗabi'un mu da mu'amalolinmu.

Ka samu labarin mutuwar wanda baka taɓa tsammani mutuwa akan sa ba yanzu, amma hakan bai zama ishara gareka ba, bai saka maka tsoron Ubangijinka ba, bai sanya ka nadama ba.

Abu na farko da ya kamata ka tambayi kanka, Shin anya kuwa ina da rabo a gobe kiyama?
Babu wani abu da ya rage wanda zai firgita ɗan Adam kamar Mutuwa, idan har aka wayi gari ka daina jin komai a lokacin da ka samu labarin mutuwa, to akwai buƙatar ka binciki kanka.

Wannan rayuwa ta yaki halak ta yaki haram, rayuwar zalunci da ƙeta, rayuwar munafunci da zanba, rayuwar ɗaukar hakki, rayuwar kisa ba gyara ba dalili, rayuwar cin amana da butulci bazasu taba kaimu ga tudun mun tsira ba.

Maza kuji tsoron Allah, mata kuji tsoron Allah, ka sani duk abinda kake aikatawa Allah yana kallon ka, ko rami ka tona ka shiga ciki ka rupe ka aikata abinda kakeso to Allah yana kallon ka, sannan duk abinda kayi wa diyar wasu kaima sai anyi da taka diyar ko kanwarka ko mahaifiyar ka da sauransu, haka kema duk abinda kikayi sai an miki! Saboda haka muji tsoron Allah mu daina aikata duk wani abunda Allah ba ya so, muyi abinda yake so domin shine zai kaimu tudun mun tsira, mu gaggauta tuba, kar mu jinkirta tuba!

Allah Ubangiji ya kiyaye mu ya bamu ikon tuba tun kamin mutuwa ta dauke mu! Ameen

🌿 YADDA AKE YIN ADU'A KAMAR YADDA MANZON ALLAH ﷺ YA KOYA1️⃣ Ka fara da yabon Allah.Annabi ﷺ ya koyar da wani mutum yadda...
09/08/2026

🌿 YADDA AKE YIN ADU'A KAMAR YADDA MANZON ALLAH ﷺ YA KOYA

1️⃣ Ka fara da yabon Allah.

Annabi ﷺ ya koyar da wani mutum yadda zai yi addu'a, sai ya fara da yabon Allah da girmama Shi.

Misali:

> الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ

"Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Ubangijin talikai."

2️⃣ Ka yi salati ga Manzon Allah ﷺ.

Misali:

> اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ

"Ya Allah, Ka yi salati ga Muhammad ﷺ."

3️⃣ Sannan ka roƙi Allah abin da kake buƙata. 🤲

Ka roƙe Shi cikin ƙasƙantar da kai, tsoronSa da yaƙini. Ka roƙi Allah komai, babba ko ƙarami.

Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:

> ادْعُونِي أَسْتَجِبْ لَكُمْ

"Ku roƙe Ni, Zan amsa muku."

📖 Suratu Ghafir: 60

4️⃣ Ka zaɓi kyawawan Sunayen Allah da s**a dace da buƙatarka.

Misali:

🤲 Yā Ghaffār — idan kana neman gafara.
🤲 Yā Raḥmān, Yā Raḥīm — idan kana neman rahama.
🤲 Yā Razzāq — idan kana neman arziki.
🤲 Yā Hādī — idan kana neman shiriya.

5️⃣ Ka yi salati ga Annabi ﷺ bayan addu'ar.

Wannan yana daga cikin ladubban addu'a da s**a zo a Sunnah.

📚 Sahih al-Bukhari da Sahih Muslim; Abu Dawud da At-Tirmidhi.

🤲 Allah Ya karɓi addu'o'inmu, Ya ba mu abin da yake alheri a gare mu a duniya da Lahira. Āmīn.

*ME MUMINI YAKE GANI A LOKACIN MUTUWARSA?*"Mumini zaiyi burin haɗuwa da Allah a lokacin mutuwarsa, kuma shima Allah zai ...
08/08/2026

*ME MUMINI YAKE GANI A LOKACIN MUTUWARSA?*

"Mumini zaiyi burin haɗuwa da Allah a lokacin mutuwarsa, kuma shima Allah zai yi burin haɗuwa dashi, domin haƙiƙa shi muminin ya ƙarar da rayuwarsa ne wajen yiwa Allah da manzonsa biyayya ne dalilin hakan sai yasa Allah maɗaukakin sarki yayi masa kyakkyawar tarba"

"Amma kuwa wanda ya ƙarar da rayuwarsa wajen saɓawa Allah da manzonsa, to haƙiƙa yana cikin haɗari da fargabar da bai taɓa shiga cikin irinta ba anan duniya"

"Manzon Allah ﷺ, yace: shi mumini idan mutuwa ta bijiro masa, lallai ana yi masa bushara da samun yardar Allah da karamarsa ne, babu wani abinda yafi soyuwa a gareshi face sai abinda yake a gabansa, yana son haɗuwa da Allah, kuma shima Allah yana son haɗuwa dashi"
Bukhari ne ya

*KAFIN KA KWANTA BACCI… 🤲*Kada ka kwanta ka manta da Allah.🕊️ Ka yi alwala idan za ka iya.📖 Ka karanta addu’o’in kwanciy...
07/08/2026

*KAFIN KA KWANTA BACCI… 🤲*

Kada ka kwanta ka manta da Allah.

🕊️ Ka yi alwala idan za ka iya.
📖 Ka karanta addu’o’in kwanciya barci na Sunnah.
📖 Ka karanta Ayoyi biyu na ƙarshe na Suratul-Baƙara.

*Manzon Allah ﷺ ya ce:*

“Duk wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshe na Suratul-Baƙara da dare, sun isar masa.”
📚 Sahih al-Bukhari: 5051

🤲 Ka kwanta da zikiri, ka kwanta da tawakkali, ka kwanta kana neman tsari daga Allah.

Allah Ya tsare mu da iyalanmu daga dukkan sharri. 🤲❤️

07/08/2026

*🕌GORON JUMA'A🕌*
*Ka tuna cewa duniya ba gidan dawwama ba ce. Saboda haka, ka yi wa kanka tanadin abin da zai amfane ka a gidan gaskiya.*

*A kullum, ka yi ƙoƙarin gyara dangantakarka da Allah, ka kyautata wa mutane, kuma ka yawaita ayyukan alkhairi. Lokaci yana tafiya, amma sakamakon ayyukanmu shi ne abin da zai kasance tare da mu har abada.*

*Allah Ya sa mu cika da imani, Ya sa mu gama da duniya lafiya, Ya kuma kyautata ƙarshenmu. Amin. 🤲*

Ya Allah, Ka ciyar da mu daga halal a cikin rayuwarmu. Ka sanya albarka a cikin dukkan al'amuranmu. Ka biya mana dukkan ...
07/08/2026

Ya Allah, Ka ciyar da mu daga halal a cikin rayuwarmu. Ka sanya albarka a cikin dukkan al'amuranmu. Ka biya mana dukkan buƙatunmu na alheri.

Ya ubangiji, Ka ci gaba da kare mu daga sharrin masu sharri, mutane da aljannu. Ka tsare mu daga abin kunyar duniya da na Lahira.

06/08/2026

TUNATARWA
"Gada a manta da yawaita yima ANNABI ﷺ Salati acikin wannan Daren na juma'a mai albarka"

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Da'awatussunnah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share