23/10/2026
Rana ba kawai wata kwalliya ce mai haske a sararin samaniya ba
ita ce babban ginshiƙin tsarin duniyarmu wato (solar system).
Rana tana ɗaukar kusan kashi 99.8% na dukkan nauyin tsarin duniya, yayin da sauran abubuwa k**ar duniyoyi, watanni, ƙwayoyin taurari (comets), duwatsu (asteroids), da ƙananan duniyoyi (dwarf planets) duk sai an haɗa su duka sannan zasu kai 0.2%.
Wannan bambancin ne yasa Rana take da cikakken iko da nauyin janyo komai da yake a acikin zagayenta.
ba don ƙarfinta da Allah ya saka mata ba, na janyo abubuwa (gravity), da duniyoyi sun warwatse ba tare da tsari ba acikin sararin samaniya.
Wannan karfin ne kesa duniya take zagaye rana a daidai, tana kiyaye lokutan shekara, yanayi, da rayuwa domin su kasance a dai_dai.
Haka kuma yake ga sauran duniyoyi, watanni, da ƙananan taurari k**ar comets da asteroids, duk suna bin dokar wannan jan na Rana.
Rana ce kuma tushen dukkan mak**ashi a tsarin duniya domin a cikin cikinta nuclear fusion ke gudana inda hydrogen ke haɗuwa don samar da haske da zafi, Wannan haske da zafi ne ke bawa Duniya rai, shi yake motsa iska, teku, da tsarin photosynthesis wanda tsirrai ke amfani da shi.
Duk da cewa duniyoyi da watanni suna burge mu, Rana ce ke jagorantar komai da ƙarfin nauyinta da haskenta da ubangiji ya samar mata
Fahimtar Rana na nuna yadda tsarin duniya yake cike da daidaito da hikima, ƙaramin sauyi a nauyin Rana ko haskenta zai iya canza hanyar duniyoyi ko ma yanayin duniyar gaba ɗaya
Wannan yana nuna cewa Rana ba kawai haske bace ita din wani ginshiƙi ce dake riƙe tsarin duniyar mu baki ɗaya.
Duka a cikin ƙarfin ikon Allah 😍💯
Don haka, a lokacin da ka kalli Rana, ka tuna cewa kusan komai a cikin tsarin duniya yana zagayena, ta fuskar zahiri da ma’ana.
Allah yasa mu wanye lafiya
Sir Wisdom