29/08/2026
🚨🤲🏽 KANO TO KAOLACK — Ya Himmar Shehu, Ki Ceto Masoyan Shehu! 🌹
Masoyan Shehu da s**a tashi daga Kano zuwa Senegal domin halartar Maulidin Shehu Ibrahim Inyass (RTA), sun samu matsala a hanya a wani daji mai hatsari a ƙasar Mali. 🇲🇱
Direban ya manta hanya, har ya shigar da su cikin wani daji mai nisa, inda motarsu ta makale. Ana ta ƙoƙarin fitar da motar tun tsawon kwana ɗaya, amma abin ya ci tura. 🚐😢
A wurin babu Network, don haka ba a san inda suke ba, kuma ba a samu damar tuntuɓar su ba sai yau. Wasu daga cikin masoyan da ke kan hanya, waɗanda motocinsu ba su samu matsala ba, sun sami wuri sun tsaya a bakin t**i domin idan waɗanda suke cikin dajin s**a fito, su haɗu da su su ci gaba da tafiya tare. 🤲🏽❤️
Gashi kuma ba su san sunan dajin ba, Network baya aiki, bare a iya gano inda suke. Masoyan suna ta ƙoƙarin haƙa ƙasar da ta riƙe tayoyin motar, domin a samu damar yin reverse ko motar ta koma baya zuwa kan kwalta, amma abin ya ƙi tun jiya. 😢🤲🏽
Shehu, ga masoyanka nan! 😭❤️
Ba su san kowa ba, ba su san komai ba, sai kai da Allah. 🤲🏽
🌿🤲🏽 Yanzu haka suna cikin daji suna ta zikiri. ❤️🌹
Ƴan kaɗan ne kawai s**a damu da gyaran motar, sauran kuma Shehu kawai s**a sani. 🤲🏽❤️
🌹 Ya Himmar Shehu, ki ceto masoyan Shehu!
🤲🏽 Ya Gausun ƙarfi da buwaya, Shehu Gausun iko da kaɗaita ka ceto msy, Allah ka kubutar da su cikin ƙoshin lafiya, ka dawo da su kan hanya lafiya.
Ya Allah, muna roƙonKa Ka kuɓutar da masoyan a yau ɗin nan, bisa albarkar Shehu Ahmadu Tijjani (RTA). 🤲🏽❤️🌹
Amin Ya Rabbal Alamin. 🤲🏽