Usmaniyya Nasarawa kaduna

Usmaniyya Nasarawa kaduna Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Usmaniyya Nasarawa kaduna, Photographer, AA31 Nasarawa Road Nasarawa kaduna, Kaduna.

11/06/2026
11/06/2026
11/06/2026

Ƴan Takarar APC 76 Sun Kai Jam’iyya Kotu Kan Zaɓen Fidda Gwani na Majalisar Dokokin Zamfara

Akalla ƴan takara 76 masu neman kujerun Majalisar Dokokin Jihar Zamfara a ƙarƙashin jam’iyyar APC sun shigar da ƙara a kotu ranar Laraba, inda suke ƙalubalantar sakamakon zaɓen fidda gwani na majalisar dokokin jihar.

Masu ƙarar sun zargi jam’iyyar da aikata wasu kura-kurai da rashin bin ƙa’ida a yayin gudanar da zaɓen fidda gwani, lamarin da s**a ce ya haifar da rashin adalci wajen fitar da waɗanda za su wakilci jam’iyyar a zaɓen 2027.

Sun buƙaci kotu ta binciki yadda aka gudanar da zaɓen tare da ɗaukar matakin da ya dace domin tabbatar da adalci da bin dokokin jam’iyya da na zaɓe.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan ƙarar da aka shigar ba.

10/06/2026
10/06/2026

Wasu Hanyoyi Gwamnati zata bi wajen kawo karshen masu tallafawa Yan Bindiga da bata gari dake cikin Al'umma masu taimakawa ƴan Ta'adda dake cikin daji ?

10/06/2026

Ƙungiyoyin Fararen Hula Za Su Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zangar Ƙasa A Ranar 12 Ga Watan Yuni Kan Tsaro Da Tsadar Rayuwa

Gamayyar ƙungiyoyin fararen hula da masu fafutuka, ƙarƙashin jagorancin fitaccen Lauya, Femi Falana, sun shirya gudanar da gagarumar zanga-zangar ƙasa a ranar 12 ga Yuni, 2026 domin nuna adawa da matsalar rashin tsaro da tsadar rayuwa a Najeriya, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.

A cewarsu, manufar zanga-zangar ita ce matsa wa gwamnati lamba ta ɗauki matakan gaggawa wajen ceto waɗanda ke hannun masu garkuwa da mutane da kuma sake duba manufofin tattalin arziƙin gwamnatin Tinubu da suke ganin sun ƙara jefa jama'a cikin ƙunci.

Ranar 12 ga watan Yunin kowace shekara ita ce ranar da gwamnati ta ware a matsayin ranar Dimokaraɗiyya, sai dai a cewar masu shirin zanga-zangar ba murna ce ta kamaci ranar ba.

Address

AA31 Nasarawa Road Nasarawa Kaduna
Kaduna
800251

Telephone

+2348028290447

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Usmaniyya Nasarawa kaduna posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Usmaniyya Nasarawa kaduna:

Shortcuts

Share

Category