17/08/2026
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana sake zaɓen gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun a matsayin wata alama cewa dimokuraɗiyya za ta ci gaba da bunƙasa a Nijeriya.
Shugaban wanda ya bayyana wannan a wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce shi ya taya gwamnan murna a wata tattaunawar da s**a yi ta wayar salula.
Gwamna Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord (A) ya ci galaba kan Bola Oyebamiji na jam’iyyar APC da Najeem Salam na jam’iyyar ADC.
Ademola ya samu ƙuri’u 511,067 inda Oyebamiji ya samu 444,815 yayin da Salam ya samu ƙuri’u 17, 180.
“Sake zaɓen Gwamna Ademola Adeleke a zaɓen da aka kamalla na Osun wani tabbaci ne cewa dimokuraɗiyya za ta ci gaba da bunƙasa a ƙasarmu a ƙarƙashin gwamnatin jam’iyyar APC,” kamar yadda Tinubu ya bayyana a saƙon