14/08/2026
Masallacin Al-Ghamama, Madinar Manz0n Allah (S.A.W)
Ɗaya daga cikin wuraren tarih! masu girman daraja a Madina.
Wannan shi ne Masallacin Al-Ghamama, wurin da aka ruwaito cewa Manzon Allah ﷺ ya yi Sallar Idi, kuma ya yi addu'ar neman ruwan sama, Allah Ya saukar da gajimare ya ba mutane rahama.
Yayin da na tsaya a wannan wuri, zuciyata ta tuna cewa tarihin Musulunc! ba labari ba ne kawai—gaskiya ce da ta faru a irin waɗannan wurare.
Wata rana watakila kai ma Allah zai ba ka ikon tsayawa a nan, ka ɗaga hannuwanka cikin tawali'u, kana roƙonSa alheri. Kada ka daina addu'a, domin Allah Mai amsa addu'a ne.
Ya Allah, kamar yadda Ka ba ni damar ganin wannan wuri mai albarka, Ka ba duk wanda yake karanta wannan rubutu damar ziyartar Madina da Makkah cikin lafiya da imani.
Ka karɓi ibadunmu, Ka yafe mana zunubanmu, Ka haɗa mu da ManzonKa ﷺ a Aljannar Firdausi.