25/09/2026
YABON GWANI YA ZAMA DOLE!
Abba Sani Pantami ka zama abin alfahari ga Anguwar Pantami Malam Kuri da ma al’ummar Gombe baki ɗaya.
A lokacin da Anguwar Pantami Malam Kuri ta shiga cikin matsalar wutar lantarki sakamakon lalacewar transformer, Professor Isa Ali Pantami ya bayar da kuɗin da za a gyara transformer ɗin domin dawo da wutar lantarki ga al’umma, ta hannun Abba Sani Pantami.
Muna miƙa godiya ta musamman ga Prof. Isah Ali Ibrahim Pantami bisa wannan babban tallafi da ya bayar domin taimakon al’ummar Anguwar Pantami Malam Kuri. Haka kuma, muna godiya ga Abba Sani Pantami bisa yadda ya karɓi wannan nauyi tare da isar da tallafin cikin mutunci da amana.
Wannan ba ƙaramin abu ba ne, musamman ganin yadda matsalar wutar lantarki ta shafi rayuwar al’umma.
Haka nan muna godiya ga duk wanda ya bayar da gudummawarsa wajen ganin an samu mafita ga wannan matsala. Allah Ya saka wa kowa da mafificin alheri.
Allah Ya saka wa Prof. Isah Ali Ibrahim Pantami da alheri, Ya ƙara masa arziki da ɗaukaka, Ya kuma sanya wannan taimako ya zama sadaka mai gudana a gare shi. Yakuma Bashi Nasaran Zama Gomna Jihar Gombe Ameen 🤲
Abba Sani Pantami — abin alfaharin Pantami Malam Kuri.
Pantamiyya TV network global TV concept Pantami Malam Kuri Unity Forum Abba Sani Pantami Abba Hikima