19/10/2026
Me ke yawan gwara kan Kwankwaso da Atiku?
Daga:Ramlat Ahmad
Yayin da ake ta tattaunawa kan yiwuwar haɗakar manyan ƴan'adawa gabanin zaɓen 2027, rikici tsakanin manyan jagororin hamayya na ƙara haifar da koma bayan yunƙurin haɗewar ƴanhamayyar.
Musayar yawun da ta ɓarke a baya-bayan nan tsakanin jagoran kwankwasiyyar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na NDC da kuma jam'iyyar ADC na ci gaba da aza ayar tambaya kan fatan haɗewar.
A wannan wata ne sabon rikici ya ɓarke tsakanin ADC da Kwankwaso bayan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugabna ƙasa na ADC ya zargi Kwankwaso da mayar da hankali wajen s**ar Atiku Abubakar maimakon APC.
Lamarin da har ta kai ga kwamitin yaƙin neman zaɓen Atikun ya zargi Kwankwaso da taimaka wa jam'iyya mai mulki.
Sai dai Kwankwaso ya musanta zargin, yana mai cewa shi da jam'iyyarsa ko shi ɗantakarar shugaban ƙasa na jam'iyyarsa ta NDC, Peter Obi ba sa yi wa APC aiki, kuma ba za su janye wa Atiku takara ba.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a ƙarshen mako, Kwankwaso ya ce maimakon ADC ta mayar da hankali wajen nuna cancanta da ƙwarewar ɗan takararsu, suna ƙoƙarin yaɗa zarge-zarge cewa NDC na yi wa APC aiki, ko kuma za ta janye wa ADC.
Kodayake Atiku da Kwankwaso sun taɓa yin aiki tare a ƙarƙashin jam'iyyun siyasa daban-daban, dangantakarsu ta fuskanci ƙalubale a lokuta da dama, musamman kan batun shugabanci, rabon iko da kuma wanda zai jagoranci ƙawancen adawa.
IMS ONLINE TV