13/07/2026
AN ƘADDAMAR DA RABON TAKIN ZAMANI KYAUTA GA AL'UMMAR ƘARAMAR HUKUMAR MULKI TA KOKO-BESSE
A yau Litinin, 13 ga Yuli, 2026, Mai Girma Shugaban Ƙaramar Hukumar Mulki ta Koko-Besse, Hon. Sirajo Usman Koko (Dan Gwaggo), ya jagoranci ƙaddamar da rabon buhunan taki 3,056 da Mai Girma Gwamnan Jihar Kebbi, Comrade Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu), ya ware domin tallafa wa manoman ƙaramar hukumar.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa an tsara rabon takin ne ta runfunan zaɓe domin tabbatar da adalci da gaskiya. Saboda haka, ba a ware takin ga ƙungiyoyi, ma'aikata, sarakuna, shugabanni, 'yan siyasa ko 'yan jarida ba. Kowane mai hakki zai karɓi rabonsa ne a runfar zaɓensa k**ar sauran al'umma.
A jawabinsa, Hon. Sirajo Usman Koko ya tabbatar da cewa gwamnatin ƙaramar hukumar ta aiwatar da umarnin Mai Girma Gwamna ba tare da ƙari ko ragi ba. Ya kuma bayyana cewa an raba dukkan takin da aka kawo zuwa runfunan zaɓe ba tare da cire ko buhu guda ba.
Domin sauƙaƙa aikin rabon, gwamnatin Ƙaramar Hukumar Koko-Besse ta ɗauki nauyin jigilar dukkan takin zuwa mazabu da runfunan zaɓe da kuɗinta, domin kauce wa duk wata matsala ta sufuri ko wani ƙarin kuɗi ga al'umma.
A madadin Mai Girma Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu, Hon. Garba Umar Dutsin Mari, wakilinsa Hon. Yahaya Bello Koko (Sarkin Gabas) ya yi bayanin tsarin rabon, inda ya jaddada cewa manufar ita ce tabbatar da cewa tallafin gwamnati ya isa ga waɗanda aka tanada wa cikin gaskiya da adalci.
Taron ya samu halartar wakilan Masarautar Koko-Besse, shugabannin APC, kansiloli, hakimai, jami'an tsaro, wakilan 'yan majalisu da dimbin al'ummar Ƙaramar Hukumar Koko-Besse.
Abin lura shi ne, an raba buhunan taki 3,056 zuwa runfunan zaɓe 191, inda kowace runfa ta samu buhu 16, abin da ya tabbatar da daidaito wajen rabon.
Haka kuma, an bayyana cewa shugaban kwamitin rabon taki na kowace Ward shi ne Kansilan Ward ɗin, yayin da Shugaban APC na Ward yake matsayin Sakataren Kwamitin tare da sauran mambobi. Don haka, duk wata matsala da ta taso a kowace runfa tana ƙarƙashin jagororin wannan runfar.
An kammala taron cikin kwanciyar hankali da nasara.
Allah Ya saka wa Mai Girma Gwamnan Jihar Kebbi, Comrade Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu), da alheri, Ya ƙara masa lafiya da nasara. Haka kuma Allah Ya ƙara wa Hon. Garba Umar Dutsin Mari da Hon. Sirajo Usman Koko (Dan Gwaggo) hikima da ƙarfin ci gaba da yi wa al'umma hidima.
Ciroman Koko Media Team
13/07/2026